Da duminsa: An kama limamin masallaci da kokon kan mutum

Da duminsa: An kama limamin masallaci da kokon kan mutum

- 'Yan sandan jihar Osun sun cafke wani limamin masallaci dauke da kokon kan mutum

- Kwamishinan 'yan sandan jihar, Wale Olokode ya tabbatar da aukuwar lamarin a Osogbo

- Tuni limamin ya amsa laifinsa tare da bayyana cewa tsafi za su yi da kokon kan mutum

Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta cafke wani limamin masallaci dauke da kokon kan dan Adam a unguwar Iwo ta jihar Osun.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Wale Olokode ya tabbatar da aukuwar lamarin .

An mika wanda ake zargin hedkwatar 'yan sanda ta Iwo inda za a wuce da shi sashin binciken na musamman ta jihar da ke Osogbo don cigaba da bincike.

KU KARANTA: Shugaba Buhari a 2021: Cikakken tarihi, dukiyar da ya tara, shekaru, ilimi da iyalinsa

Da duminsa: An kama limamin masallaci da kokon kan mutum
Da duminsa: An kama limamin masallaci da kokon kan mutum. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

Tuni dai limamin masallacin ya amsa laifinsa inda yace yana kawo kan mutun ne a kan Naira dubu 20.

"Da gaske an kama ni da kan mutum. Na siyo daga wani wuri ne domin amfanin tsafin kudi da za mu yi. Na siya a kan Naira dubu 20," In ji shi.

Kwamishina Olokode ya tabbatar da cewa an damko wasu mutane da ake zarginsu da hannu a lamarin.

KU KARANTA: Masoyan da suka adana N4.5m tsawon shekaru 5 sun hada shagalin bikinsu mai kayatarwa da kudin

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Katsina sun kama wani Kabiru Bashir mai shekaru 27 da Sadiq Ashiru mai shekaru 30, duk 'yan karamar hukumar Danbatta dake jihar Kano bisa zargin damfarar mutane ta waya da sunan su Aljanu ne.

Kakakin 'yan sandan jihar, Gambo Isah ya sanar da hakan a wata takarda, wacce yace alhakin jama'a ne ya kama su bayan sun amshi katin bankin wata Rabi'atu Garba ta karamar hukumar Mani dake jihar Katsina.

"Wadanda ake zargin, sun fara kiranta ta waya suna ce mata su Aljanu ne, inda suka bukaci ta basu katin bankinta da lambarsa ta cirar kudi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel