Hotuna: 'Aljanun Kano' da suka dade suna damfara sun shiga hannun hukuma a Katsina

Hotuna: 'Aljanun Kano' da suka dade suna damfara sun shiga hannun hukuma a Katsina

- 'Yan sandan jihar Katsina sun kama wasu samari 2 da laifin damfara ta waya

- Samarin suna ikirarin su Aljanu ne, daga nan su tattara kudaden mutum su tsere

- Dubunsu ta cika ne bayan sun amshi katin bankin wata Rabi'atu Garba 'yar Katsina

'Yan sandan jihar Katsina sun kama wani Kabiru Bashir mai shekaru 27 da Sadiq Ashiru mai shekaru 30, duk 'yan karamar hukumar Danbatta dake jihar Kano bisa zargin damfarar mutane ta waya da sunan su Aljanu ne.

Kakakin 'yan sandan jihar, Gambo Isah ya sanar da hakan a wata takarda, wacce yace alhakin jama'a ne ya kama su bayan sun amshi katin bankin wata Rabi'atu Garba ta karamar hukumar Mani dake jihar Katsina.

"Wadanda ake zargin, sun fara kiranta ta waya suna ce mata su Aljanu ne, inda suka bukaci ta basu katin bankinta da lambarsa ta cirar kudi.

Hotuna: 'Aljanun Kano' da suka dade suna damfara sun shiga hannun hukuma a Katsina
Hotuna: 'Aljanun Kano' da suka dade suna damfara sun shiga hannun hukuma a Katsina. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Mashahurin mai kudin duniya, Elon Musk, ya tafka asarar $14 biliyan a rana daya

"Wadanda ake zargin, sun yi ikirarin tallafa mata da N1,000,000 ta asusun bankinta, kuma sun umarce ta da taje bankinta, UBA don tayi wasu gyare-gyare.

"Yayin da ta fara zarginsu da damfara, sai tayi hanzarin sanar da 'yan sanda a ofishinsu na birnin Katsina. Da bincike yayi bincike, sai aka bankado su," kamar yadda takardar tazo.

Hotuna: 'Aljanun Kano' da suka dade suna damfara sun shiga hannun hukuma a Katsina
Hotuna: 'Aljanun Kano' da suka dade suna damfara sun shiga hannun hukuma a Katsina. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

Isah ya ce mai laifin ya amsa laifinsa, inda yace sun damfari mutane da dama ta wannan hanyar.

A cewarsa, an samu an kwace wata farar mota kirar Honda mai lamba JHMGD173025215012, da katinan banki guda biyu na wani Kabiru Bashir, wayoyi 4, da kuma N126,000 daga hannunsu.

Isah ya ce za a tura su kotu da zarar an kammala bincike.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon Regina Daniels tana gwangwaje mahaifiyarta da motar alfarma A wani labari na daban, wasu mazauna kauyukan Bakin kogi da Narido sun tarar da ajalinsu bayan da 'yan bindiga suka kai musu hari a karamar hukumar Kauru ta jihar kaduna.

Dakarun sojin rundunar Operation Safe Haven sun sanar da gwamnatin jihar kaduna batun wannan hari a ranar Talata, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, ya ce dakarun sojin sun gaggauta zuwa bayan kiran gaggawan da suka samu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel