Gwamnatin tarayya da gwamnonin Kudu sun cimma matsaya kan Amotekun

Gwamnatin tarayya da gwamnonin Kudu sun cimma matsaya kan Amotekun

Gwamnatin tarayya da gwamonin jihohin Kudu maso Yamma sun cimma matsaya a kan rundunar tsaro da Yammacin kasar da ake yi wa lakabi da Operation Amotekun.

Babban mai taimakawa mataimakin shugaban kasa na musamman, Laolu Akande ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.

Sai dai bai bayar da cikakken bayanin matsayar da suka cimma ba.

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo da gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma sun gana a fada Aso Villa a Abuja a ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa mukasudin taron shine tattaunawa kan rundunar tsaron ta Amotekun da gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ya saba wa doka.

DUBA WANNAN: Sokoto: Hukuncin kotun koli ba zai rage mu da komai ba - Wamakko

Gwamnonin da suka hallarci taron sun hada da Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, Kayode Fayemi na Ekiti da Gboyega Oyetola na Osun.

Gwamnonin Oyo da Legas sun samu wakilcin mataimakansu.

Kakakin mataimakin shugaban kasar ya ce an kira taron ne saboda gwamnonin sun nemi ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari kan takadamar batun na Amotekun.

Akande ya ce an bukaci mataimakin shugaban kasa ya gana da su domin Shugaba Buhari ya tafi hallartar wani taron a kasar waje.

Sanarwar ta ce, "Gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma sun cimma matsaya a kan Amotekun" tare da cewa taron ya yi armashi kuma an warware matsalar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164