Dakarunmu sun kashe Sojojin ta’dda 64 a cikin mako daya a Jihar Yobe inji DHQ
- Jami’an tsaro sun kashe Sojojin Boko Haram a jihar Yobe a watan Junairu
- Sojojin sun yi nasarar karbe makamai daga hannun ‘yan ta’addan a Yobe
- Hedikwatar Jami’an tsaro ta bada wannan sanarwa ta bakin John Enenche
Hedikwatar jami’an tsaro ta kasa ta ce ‘yan ta’adda 64 ta kashe a jihar Yobe a cikin mako guda a ba-ta-kashin da su kayi da dakarun sojoji.
Punch ta rahoto kakakin dakarun Najeriya, Janar John Enenche ya na cewa ‘yan ta’addan sun gamu da ajalinsu a karamar hukumar Gujba, Yobe.
Manjo Janar ya kuma bayyana cewa dakarun Operation Tura Takai Bango sun hallaka ‘ya ta’adda a yankin Gonan Kaji a kan hanyar Buni-Yadi.
Da yake magana da ‘yan jarida a ranar Alhamis, 14 ga watan Junairu, jami’in ya ce an fatattaki ‘yan ta’addan ne tsakanin 7 zuwa 13 ga watan nan.
KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun kona coci, sun hallaka mutane a Chibok
A wajen wannan hari, jami’an sojojin sun yi nasarar karbe alburusai da bindigogi da motocin yaki daga hannun ‘yan ta’ddan kungiyar ISWAP.
“An hallaka wasu yan ta’adda, wasu da-dama sun tsere da harbin bindigogi, yayin da aka samu motar yaki da makamai da harsashai.” Inji Enenche.
“A wannan rana kuma, sojoji sun yi arba da wasu ‘yan ta’addan Boko/ISWAP a kauyen Gonan Kaji da ke kan hanyar Damaturu-Buni Yadi, Yobe.”
“A harin, an kashe ‘yan ta’dda 30, sannan jami’an sojoji sun samu makamai da harsashai.”
KU KARANTA: Boko Haram sun sace ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya
A ranar 10 ga watan Junairu, sojojin kasa sun hallaka wasu ‘yan ta’adda shida a garin Kafa, karamar hukumar Dambao, a nan ma an samu makamai.
Haka zalika an kashe sojojin Boko Haram a Goniri da Gorgi a Gujba da Damaturu inji jami’in.
Kwanaki kun ji cewa wasu miyagun ‘yan ta’adda da ake zargin cewa ‘yan kungiyar nan ta Boko Haram ne sunyi mummunar barna a kauyen Geidam a Yobe.
Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa wadannan ‘yan ta’adda sun fasa shagunan Bayin Allah, sun saci kayan abinci a garin na tsohon gwamnan jihar Yobe.
Bayan haka, an sace Hakimin garin Maganna da ke karkashin masarautar Ngazargamu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng