Boko Haram sun sace ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu
- Boko Haram sun sace wani Ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya a hanyar Maiduguri a safiyar Asabar
- An kama ma'aikacin ne tare da wasu mutum da aka sake su daga baya
- Majiya ta ruwaito cewa maharan sun kai hari ne kan matafiyan
'Yan ta'addar Boko Haram sun sace wani babban mataimaki na kariya a Hukumar Kula da' Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Alooma, a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, Jihar Borno.
KU KARANTA: Jami'an yan sanda sun dakile harin yan bindiga, sun ceto wanda aka sace
PRNigeria ta tattaro cewa maharan sun kaiwa wasu ayarin matafiya hari a kusa da kauyen Matari tsakanin Minok zuwa hanyar Jakana inda aka yi garkuwa da Alooma da misalin karfe 8.30 na safiyar Asabar.
Wata majiya ta bayyana cewa maharan wadanda suka fito sanye da kayan sojoji sun sanya shingen kan hanya a kan babbar hanyar da motocin Hilux guda uku da babura.
Majiyoyin sun ce: “Yayin da ake binciken fasinjojin, Idris ya yi kokarin jefa katin shaidarsa amma ana kan haka, sai daya daga cikin maharan ya ganshi. Daga nan aka nemi ya sauka daga motar tare da wasu fasinjoji biyu, yayin da aka nemi sauran fasinjojin da su ci gaba da tafiya.
KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kashe shugabanni 2 a jihar Kaduna
"Daga baya an saki fasinjojin biyu a kan cewa su talakawa ne sosai kuma ba su da wani amfani da za a sace su."
A wani labarin, Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum a ranar Asabar ya ziyarci mafarauta shida da a halin yanzu suke karbar kulawar masana kiwon lafiya a asibitin koyarwa da ke Maiduguri.
Mafarautan sun samu miyagun raunika sakamakon dashen abu mai fashewa da mayakan Boko Haram suka yi wanda ya tashi da mafarautan yayin da suke sintiri a dajin Sambisa.
Kusan mafarauta bakwai ne a take suka mutu yayin da wasu 16 suka samu miyagun raunika.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng