'Yan fashi da makami sun bindige wani bawan Allah a garin Kano

'Yan fashi da makami sun bindige wani bawan Allah a garin Kano

- Wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan fashi ne sun kashe wani Mustapha Abubakar, mazaunin jihar Kano

- Al'amarin ya faru ne da safiyar Alhamis, 14 ga watan Janairu, kamar yadda dan uwansa ya tabbatar

- A cewarsa, bayan dawowar Abubakar daga masallaci bayan sallar Asuba ne 'yan fashin suka harbe shi a gidansa

Har yanzu, harkokin tsaro sai kara tabarbarewa suke yi, don da safiyar Alhamis, 14 ga watan Janairu wasu mutane, da ake zargin 'yan fashi ne suka kashe wani Mustapha Abubakar a jihar Kano.

Dan uwan Abubakar ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda yace sun harbi dan uwansa ne da safiyar Alhamis.

Kamar yadda yace, Abubakar yana hanyar komawarsa gida daga masallaci mummunan lamarin ya auku.

KU KARANTA: Masoyan da suka adana N4.5m tsawon shekaru 5 sun hada shagalin bikinsu mai kayatarwa da kudin

'Yan fashi da makami sun bindige wani bawan Allah a garin Kano
'Yan fashi da makami sun bindige wani bawan Allah a garin Kano. Hoto daga Sen Auwal Mashall
Asali: Facebook

Kamar yadda ya wallafa;

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un... 'Yan fashi sun kashe kawuna yau bayan ya idar da sallar Asuba a gidansa dake Kano. Mustapha Abubakar, Ubangiji ya ji kanka, ya kuma gafarta maka. Kowa lokaci yake jira!!!"

KU KARANTA: Liyafar badala: 'Yan sanda sun damke samarin da ake da shiryawa a Bauchi

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Katsina sun kama wani Kabiru Bashir mai shekaru 27 da Sadiq Ashiru mai shekaru 30, duk 'yan karamar hukumar Danbatta dake jihar Kano bisa zargin damfarar mutane ta waya da sunan su Aljanu ne.

Kakakin 'yan sandan jihar, Gambo Isah ya sanar da hakan a wata takarda, wacce yace alhakin jama'a ne ya kama su bayan sun amshi katin bankin wata Rabi'atu Garba ta karamar hukumar Mani dake jihar Katsina.

"Wadanda ake zargin, sun fara kiranta ta waya suna ce mata su Aljanu ne, inda suka bukaci ta basu katin bankinta da lambarsa ta cirar kudi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng