Ana rikici tsakanin Gwamnan jihar Oyo Makinde da Mataimakinsa Olaniyan

Ana rikici tsakanin Gwamnan jihar Oyo Makinde da Mataimakinsa Olaniyan

- Ana samun matsala tsakanin Seyi Makinde da mataimakinsa, Rauf Olaniyan

- Wasu na kukan Gwamnan bai taba mikawa Olaniyan mulki da ba ya nan ba

- Amma Gwamnan da Mataimakin na sa sun musanya cewa sun samu sabani

Alakar gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da kuma mataimakinsa, Rauf Olaniyan, ta cabe shekaru biyu bayan ‘yan siyasar sun lashe zaben 2019.

Wata majiya ta shaidawa jaridar The Nation cewa maganar takarar 2023 ce ta raba kan ‘yan siyasar.

A lokacin da Seyi Makinde yake kokarin cika alkawuran da ya dauka domin ya samu zarcewa a kan mulki, mataimakinsa ya na harin takara a 2023.

Burin Rauf Olaniyan na zama gwamna a lokacin da mai gidansa bai gama cinye wa’adinsa ba shi ne ya ke neman barka gidan gwamnatin jihar Oyo.

KU KARANTA: Buhari ya rabawa Gwamnoni N123bn, Tambuwal ya samu N6bn

Bangaren mataimakin gwamna, Rauf Olaniyan, suna ikirarin cewa mai girma gwamna Makinde ba ya tafiya tare da su wajen gudanar da mulkinsa.

Majiyar ta ce gwamnan ya musanya duk wani zargi da ake yi na samun rashin jituwa, ya ce akwai ayyukan da mataimakin na sa yake jagoranta a jihar.

Shi ma mataimakin gwamnan ta bakin Omolere Omoetan, ya ce rade-radin da ake yi ba gaskiya ba ne.

A ranar Laraba, 13 ga watan Junairu, 2020, Rauf Olaniyan, ya kara tabbatar da cewa nauyin da ke kansa shi ne ya hada-kai, ya yi aiki da gwamna Makinde.

KU KARANTA: Hukumar INEC tana aiki domin inganta nagartar zaben 2023

Ana rikici tsakanin Gwamnan jihar Oyo Makinde da Mataimakinsa Olaniyan
Seyi Makinde da Rauf Olaniyan Hoto: thenationonlineng.net
Source: UGC

A lokacin da gwamnan ya ziyarci wani wurin killace masu cutar COVID-19, hadiman mataimakinsa sun koka cewa ba a ba Olaniyan rikon kwarya.

Akwai lokacin da mataimakin gwamnan ya shiga gidan gwamnati ya iske Makinde ba ya ofis, yayi tafiya bai sani ba, kuma bai mika masa ragamar mulki ba.

A karshen 2019 kun ji yadda wasu mutane 4000 su ka tattara su ka bar APC, su ka dawo tafiyar jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Oyo tun bayan zaben da aka yi.

‘Yan siyasar sun tasirantu ne da salon mulkin gwamna Seyi Makinde. Sababbin ‘Ya ‘yan na PDP za su yi kokari wajen kassara APC a jihar Oyo a zaben 2023.

APC ta rasa wadannan magoya baya ne a yankunan Surulere da Ogo Oluwwa a garin Ogbomoso.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel