Mutane 4000 sun tattara sun bar APC, sun dawo Jam’iyyar PDP a Ogbomoso

Mutane 4000 sun tattara sun bar APC, sun dawo Jam’iyyar PDP a Ogbomoso

- Fiye da mutane 4, 000 su ka bar APC, su ka tsallako zuwa APC a Oyo

- ‘Yan siyasar sun tasirantu ne da salon mulkin Gwamna Seyi Makinde

- Sababbin ‘Ya ‘yan na PDP za su yi kokari wajen kassara APC a jihar

Yayin da wasu su ka fara shiryawa zaben 2023 tun yanzu, jam’iyyar APC ta gamu da rashi ne a jihar Oyo, dinbin magoya-bayanta sun canza sheka.

Sama da mutane 4000 su ka jefar da katinsu na zama ‘ya ‘yan jam’iyyar APC, su ka koma PDP wanda ta karbe mulki a jihar Oyo bayan zaben 2019.

Jaridar Vanguard ta bayyana cewa APC ta rasa wadannan magoya baya ne a yankunan Surulere da Ogo Oluwwa da ke cikin garin Ogbomoso, jihar Oyo.

KU KARANTA: Hon. Bago ya tsefe Buhari, ya koka da Gwamnatin APC

Da ya ke karban sababbin shigan na PDP, kantoman Surulere, Adegbite Isaiah ya ce salon-mulkin gwamna Seyi Makinde ne ya jawo masu karin jama’a.

Mista Adegbite Isaiah ya ce gwamnatinsu ta PDP a karkashin jagorancin Mai girma Injiniya Seyi Makinde, ta na kokarin ganin ta tafi da kowa a jihar.

Isaiah ya ke cewa wadannan dinbin mutane da su ka shigo tsarin PDP a yanzu za su taimaka wajen kawo cigaba a jam’iyyar da kuma daukacin jihar Oyo.

Ya ce: “Wannan cigaba ce, ganin yadda manyan ‘yan siyasa su ke shigowa jam’iyyar, kuma a zaben 2023, PDP za ta yi nasara a Ogo Oluwa da Surulere.”

KU KARANTA: Sauya-sheka: Buhari ya yi magana a kan Gwamnan Ebonyi

Mutane 4000 sun tattara sun bar APC, sun dawo Jam’iyyar PDP a Ogbomoso
Gwamna Seyi Makinde Hoto: @SeyiMakinde
Asali: Twitter

Tsofaffin ‘yan majalisa irinsu Peter Olusegun Oyetunji da Sunday Makanjuola suna cikin tawagar wadanda su ka rabu da jam’iyyar APC, su ka dawo PDP.

‘Yan siyasar da su ka yi sallama da APC sun sha alwashin ba PDP nasara a zabukan jihar.

Kamar yadda ku ka samu labari a tsakiyar makon nan, gwamna Udom Emmanuel ya karyata rahoton da ke yawo na facaka da biliyoyin Akwa-Ibom.

Ana zargin Gwamnan na PDP da Sakatarensa da badakalar fiye da Naira biliyan 10 a 2019.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng