Hotuna da bidiyon Regina Daniels tana gwangwaje mahaifiyarta da motar alfarma

Hotuna da bidiyon Regina Daniels tana gwangwaje mahaifiyarta da motar alfarma

- Rita Daniels ta yi murnar zagayowar ranar haihuwarta a ranar 12 ga watan Janairu

- Diyarta jaruma Regina Daniels ta gwangwajeta da kyautar sabuwar mota mai darajar miliyan 15

- Matar biloniyan ta wallafa hotuna da bidiyon lokacin tare da rako su da tausasan kalamai

Jarumar fina-finan kudu, Rita Daniels ta fada cikin matsanancin farin ciki bayan da diyarta Regina Daniels ta gwangwajeta da kyautar alfarma.

A wata wallafa da jaruma Regina tayi tare da tausasan kalami, ta bayyana motar da ta bai wa mahaifiyarta kyauta mai darajar miliyan 15 a matsayin kyautar ranar zagayowar haihuwarta.

A sakon taya mahaifiyarta murnar zagayowar ranar haihuwarta, ta bayyana cewa tana alfahari domin kuwa ta siya motar ne da kudinta wanda ta samu da kanta.

KU KARANTA: Hotunan tsuleliyar budurwa da ta zama likita sun gigita samari, suna mika kokon bararsu

Hotuna da bidiyon Regina Daniels tana gwangwaje mahaifiyarta da motar alfarma
Hotuna da bidiyon Regina Daniels tana gwangwaje mahaifiyarta da motar alfarma. Hoto daga @reginadaniels
Source: Instagram

KU KARANTA: Sallamar hafsoshin tsaro: Mutane basu hango abinda Buhari yake hange, Garba Shehu

Ta wallafa: "Mama ba zan iya baki duniya ba amma zan tabbatar da rayuwarki ta zama mai kyau. Ina alfahari da yadda na yi miki wannan kyautar da gumina. Sauran suna nan tafe."

A kwanakin kadan da suka gabata ne aka bai wa Rita Daniels sarauta a garinsu da ke jihar Delta.

Kyakyawar matar ta wallafa labarin mai dadi ga mabiyanta tare da masoyanta a shafinta na Instagram.

A wani labari na daban, fitattun mawaka da jama'a a Najeriya sun kafa wata kungiyar maza masu rowa da ake kira da Stingy Men Association of Nigeria.

Kungiyar dai babu shakka ta samu matukar karbuwa a shafukan Facebook da Twitter a Najeriya.

Mawaki Don Jazzy ba a bar shi a baya ba domin kuwa ya wallafa hoton katinsa na zama cikakken dan kungiya, lamarin da yasa jama'a suka dinga wallafawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel