Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kai hari kauyen Kaduna, sun halaka mutum 2
- Wasu 'yan bindiga sun kashe wasu mazauna kauyukan Bakin Kogi da Narido a jihar Kaduna
- Musa Garba da Yakubu Yawo suna kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Bakin Kogi ne lamarin ya faru
- Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna ya mika ta'aziyyarsa a madadin gwamnan jihar
Wasu mazauna kauyukan Bakin kogi da Narido sun tarar da ajalinsu bayan da 'yan bindiga suka kai musu hari a karamar hukumar Kauru ta jihar kaduna.
Dakarun sojin rundunar Operation Safe Haven sun sanar da gwamnatin jihar kaduna batun wannan hari a ranar Talata, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, ya ce dakarun sojin sun gaggauta zuwa bayan kiran gaggawan da suka samu.
Sun isa wurin inda suka tara da mutum biyu, Musa Garba da Yakubu Yawo a mace bayan 'yan bindigan sun dirka musu harsasai.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, wadanda 'yan bindigan suka kaiwa hari 'yan asalin kauyukan Bakin Kogi ne da Narido kuma suna hanyarsu ta zuwa kasuwar Bakin Kogi ne.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya nuna damuwarsa a kan wannan harin tare da aikewa iyalan mamatan ta'aziyya.
Gwamnan ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da sun yi bincike mai zurfi a kan aukuwar lamarin.
KU KARANTA: Magidanci ya bayyana kiyayyar da ke tsakanin mahaifiyarsa da matarsa na shekaru 7
A wani labari na daban, Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yada labarai, ya ce shugaban kasa bai sallami shugabannin tsaro ba ne saboda yana hango wata nagartarsu da 'yan Najeriya basu gani.
Shehu ya sanar da hakan a wani bakuncinsa da TVC ta karba kuma jaridar Vanguard ta ruwaito.
A yayin martani ga tambayar da aka yi masa a kan abinda ya hana Buhari ya sallami shugabannin tsaro duk da yadda ake ta bukatar yayi hakan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng