Mashahurin mai kudin duniya, Elon Musk, ya tafka asarar $14 biliyan a rana daya
- Babban mai arzikin duniya na makon jiya ya tafka babbar asara a ranar Alhamis
- Ya rasa gagarumar dukiya da ta kai dala biliyan 14, lamarin da ya matukar girgiza dukiyarsa
- A halin yanzu Jeff Bezos mai Amazon ne ya zama mutum mafi arziki a fadin duniya
Elon Musk ya sauka daga inda yake a jerin manyan masu kudin duniya. A makon da ya gabata ne aka bayyana shi a matsayin mutumin da yafi kowa kudi a duniya.
Amma kuma a rana daya ya sauka daga wannan matsayin bayan tafka asarar dala biliyan 14 da yayi, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
A halin yanzu biloniya Tesla ne zama mutum na biyu da yafi kowa kudi a fadin duniyar nan.
KU KARANTA: Magidanci ya bayyana kiyayyar da ke tsakanin mahaifiyarsa da matarsa na shekaru 7
Hannun jarinsa na bangaren hada motoci da ke aiki da wutar lantarki ya fadi da kashi 8 a ranar Litinin, 8 ga watan Janairun 2021, lamarin da ya tura Muska kasa da dala biliyan 176.2.
A cikin kankanin lokacin, mamallakin Amazon, Jeff Bezos ya zama mutumin da yafi kowa kudi a duniya kamar yadda Forbes ta kiyasta.
A halin yanzu yana kasan Bezos da dala biliyan 6 kuma dukkan dukiyarsa a halin yanzu dala biliyan 182.1 ce.
KU KARANTA: Sallamar hafsoshin tsaro: Mutane basu hango abinda Buhari yake hange, Garba Shehu
A wani labari na daban, wasu mazauna kauyukan Bakin kogi da Narido sun tarar da ajalinsu bayan da 'yan bindiga suka kai musu hari a karamar hukumar Kauru ta jihar kaduna.
Dakarun sojin rundunar Operation Safe Haven sun sanar da gwamnatin jihar kaduna batun wannan hari a ranar Talata, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, ya ce dakarun sojin sun gaggauta zuwa bayan kiran gaggawan da suka samu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng