Kyakyawar budurwa ta yi nasara a noma, ta bayyana hotunan gonarta

Kyakyawar budurwa ta yi nasara a noma, ta bayyana hotunan gonarta

- Wata kyakkyawar budurwa ta wallafa hotunanta guda 4 a gona tare da amfanin gonar a shafinta na Twitter

- Budurwar ta bayyana yadda ta fara harkar noma a 2020, inda tace noma tushen arziki ne, don haka ta riki sana'ar

- Ta bukaci abokanta na Twitter su taimaka su hada ta da wadanda za su siya amfanin gonar, don ta samu riba

Wata kyakkyawar budurwa ta bayyana hotunanta a wata katuwar gona a shafinta na kafar sada zumuntar zamani na Twitter, wanda hakan ya janyo mutane da dama suka yi ta yabon ta.

Budurwar tace noma shine tushen arziki, don haka ta yanke shawarar shiga harkar dumu-dumu a 2020. Ta bukaci jama'a su taimaka su hada ta da masu siyan hatsi.

Budurwar wacce aka fi sani da Mama_Organics, ta wallafa hotunanta guda 4 a gonar, inda ta sanar da mutane cewa tana siyar da hatsi a sari.

KU KARANTA: Femi Fani-Kayode ya samu karuwa, budurwarsa ta sunkuto masa yaro namiji

Kyakyawar budurwa ta yi nasara a noma, ta bayyana hotunan gonarta
Kyakyawar budurwa ta yi nasara a noma, ta bayyana hotunan gonarta. Hoto daga @bree_ciiku
Source: Twitter

Mutane sun yaba wa wannan sana'a ta ta a Twitter, suka ce tabbas ta yi tunani mai kyau na samun kudi.

Wani enough09652678 cewa yayi, "Kije wurare kamar asibiti, Shoprite, gidajen yari ko makarantu, ki tallata masu hatsinki.

"Ya kamata ace gwamnati tana siyan hatsi daga wurin manyan manoma irinku, suna sayar wa masu kananan karfi bisa rahusa."

Mutane da dama sun yi ta bata shawarwari iri-iri akan yadda zata bullo wa siyar da amfanin gonarta.

KU KARANTA: Sallamar hafsoshin tsaro: Mutane basu hango abinda Buhari yake hange, Garba Shehu

A wani labarai na daban, fitattun mawaka da jama'a a Najeriya sun kafa wata kungiyar maza masu rowa da ake kira da Stingy Men Association of Nigeria.

Kungiyar dai babu shakka ta samu matukar karbuwa a shafukan Facebook da Twitter a Najeriya.

Mawaki Don Jazzy ba a bar shi a baya ba domin kuwa ya wallafa hoton katinsa na zama cikakken dan kungiya, lamarin da yasa jama'a suka dinga wallafawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel