Manyan mawakan Najeriya sun shiga kungiyar marowatan maza

Manyan mawakan Najeriya sun shiga kungiyar marowatan maza

- Fitattu kuma sanannun mawaka a kasar Najeriya sun fara shiga kungiyar matsolayen samari

- Daga cikin mawakan da suka shiga kungiyar tare da bayyana katin shaidarsu akwai Don Jazzy

- A ranar Litinin ne kungiyar ta fitar da shafinta na musamman a kafar sada zumuntar Twitter

Fitattun mawaka da jama'a a Najeriya sun kafa wata kungiyar maza masu rowa da ake kira da Stingy Men Association of Nigeria.

Kungiyar dai babu shakka ta samu matukar karbuwa a shafukan Facebook da Twitter a Najeriya.

Mawaki Don Jazzy ba a bar shi a baya ba domin kuwa ya wallafa hoton katinsa na zama cikakken dan kungiya, lamarin da yasa jama'a suka dinga wallafawa.

Manyan mawakan Najeriya sun shiga kungiyar marowatan maza
Manyan mawakan Najeriya sun shiga kungiyar marowatan maza. Hoto daga @DONJAZZY
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yar bautar kasa ta sha duka, an yi mata tumbur bayan kashe saurayin da ta kwana da shi (Hotuna)

Sakamakon bunkasar da kungiyar samari marowatan ke yi a cikin kwanakin nan, kungiya ta bude shafinta na Twitter a ranar Litinin da ta gabata kuma ya matukar samun karbuwa.

Mawaki Eazi dan asalin Najeriya amma mazaunin Landan ya wallafa katinsa na shaidar zama dan kungiyar samarin marowata a shafinsa na Twitter.

Jama'a ballantana samari suna ta raha tare da kwasar nishadi a kan wannan cigaban.

Sai dai kuma, har yanzu ba a san su waye suka fara kafa kungiyar ba. Amma kuma cike da raha ake zancen kafa babban ofishin kungiyar nan gaba.

A wani labari na daban, 'yan majalisar Amurka sun fara shirye-shiryen tsige Donald Trump daga kujerar shugabancin Amurka a ranar Litinin. Sun zargi shugaban kasar da tayar da tarzoma a babban birnin Amurka.

Sannan sun zarge shi da janyo tashin hankali da rikici, da kuma yin ikirari marasa dadi akan zaben shugaban kasa da aka yi.

Sun bukaci mataimakin shugaban kasar, Mike Pence da ya yi amfani da gyararriyar doka ta 25 a kundin tsarin mulkin Amurka don ya amshi mulki daga hannun Trump.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel