Femi Fani-Kayode ya samu karuwa, budurwarsa ta sunkuto masa yaro namiji

Femi Fani-Kayode ya samu karuwa, budurwarsa ta sunkuto masa yaro namiji

- Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama ya samu karuwa

- Budurwarsa 'yar asalin kasar Morocco ta sunkuto masa kyakyawan yaro namiji

- Ya wallafa sanarwar haihuwar ne a Twitter inda ya dinga kwararawa yaron addu'a

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya samu karuwar yaro namiji.

Budurwar shi da suka dade tare 'yar asalin kasar Morocco ce ta haifa masa yaron a ranar Asabar.

A yayin sanar da haihuwar jinjirin a shafinsa na Twitter, ya rubuta, "Barkan ka da isowa duniya da na. Tabbas ka taho da albarka kuma ina matukar farin ciki da alfahari da kai. Ubangiji yayi maka albarka kuma ya tsareka."

Femi Fani-Kayode ya samu karuwa, budurwarsa ta sunkuto masa yaro namiji
Femi Fani-Kayode ya samu karuwa, budurwarsa ta sunkuto masa yaro namiji. Hoto daga @realFFK
Source: Twitter

KU KARANTA: Aljannar duniya: Bidiyon katafaren gidan Floyd Mayweather mai darajar N3.8bn

Fani-Kayode ya tabbatar da wannan ci gaban ga jaridar Premium Times a wata tattaunawar waya amma ya ki bayyana wacece mahaifiyar yaron.

Ya ce baya son kafafen yada labarai su saka ta a gaba domin kuwa alakarsu da ita ta sirri ce.

Tsohon ministan yana da yara hudu maza, 'yan uku sai yaro daya tare da tsohuwar matar shi Precious Chikwendu.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Majalisa ta fara yunkurin tsige Donald Trump daga shugabancin Amurka

A wani labari na daban, an shiga cikin tashin hankali da rudani da safiyar Litinin a ma'aikatar noma da habaka karkara dake kan titin Jabba a Iloron, lokacin da aka tsinci gawar wani darekta, Dr Khalid Ibrahim Ndaman a ofishinsa.

Vanguard ta tattaro bayanai akan yadda Dr Ndaman ne darekta na bangaren dabbobi a ma'aikatar har zuwa mutuwarsa, inda aka ga gawarsa da safiyar ranar.

An gano cewa daya daga cikin ma'aikatan ya je ofishin domin su tattauna dashi akan wani al'amari na ma'aikatar, a nan ne ya gan shi a mace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel