Yahaya Bello: APC ta kusa zama gagarumar jam'iyya da Afrika za ta yi koyi da ita

Yahaya Bello: APC ta kusa zama gagarumar jam'iyya da Afrika za ta yi koyi da ita

- Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ce kwanan nan jam'iyyar APC za ta zama shahararriyar jam'iyya a nahiyar Afirka

- A cewar gwamnan, za su koyar da har shugabannin wasu kasashe makaman da za su bi idan suna son samun nasara a zabe

- Ya kara da cewa, sai APC ta zama tamkar wata jami'a ta koyar da siyasa, wacce mutane da dama za su yi dubi da ita

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce kwanan nan jam'iyyar APC za ta zama mafi girman jam'iyya a nahiyar Afirka, The Cable ta wallafa.

Ya yi maganar ne a ranar Talata, lokacin da ake rijistar sababbin 'yan jam'iyya da kuma tabbatar da tsofaffin 'yan jam'iyyar, inda yace har wasu kasashe masu cigaba za su bukaci neman sani akan siyasa daga APC.

Ya kamata a yi taron 'yan jam'iyyar a ranar 12 ga watan Disamban 2020, amma sai aka daga zuwa mako na biyu na watan Janairun 2021.

KU KARANTA: Magidanci ya bayyana kiyayyar da ke tsakanin mahaifiyarsa da matarsa na shekaru 7

Yahaya Bello: APC ta kusa zama gagarumar jam'iyya da Afrika za ta yi koyi da ita
Yahaya Bello: APC ta kusa zama gagarumar jam'iyya da Afrika za ta yi koyi da ita. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Gwamnan jihar Kogi ya ce zai yi aiki tukuru wurin ganin jam'iyyar APC ta samu nasarori a zabukan da za a yi a kasar nan.

"Ba zama muka yi ba da ake ganin duk zaben da za a yi a jihar Kogi sai mun samu nasara. Da izinin Ubangiji, za mu yi hakan a zabukan gaba daya kasarnan," a cewarsa.

"Lokacin da muka gama duk wasu rijistar 'yan jam'iyya da kara tabbatar da tsofaffin 'yan jam'iyya a kasar nan, APC sai ta zama jam'iyyar da tafi ko wacce shahara a nahiyar Afirka, kuma sauran kasashe za su zo sanin makamar siyasa daga APC.

"Zamu koya wa 'yan uwan mu yadda ake samun nasara a zabe. Ba zan kira sunaye ba, amma zamu zama tamkar jami'a ta koyarwa akan harkar siyasa a Najeriya," ya kara da cewa.

KU KARANTA: Sallamar hafsoshin tsaro: Mutane basu hango abinda Buhari yake hange, Garba Shehu

A wani labari na daban, hukumar jami'an tsaro ta farin kaya ta bayyana cewa wasu mutane na kokarin tada rikicin addini a kasar nan a kowanne lokaci daga yanzu.

Amma a wata takarda da ta fito daga hannun kakakin hukumar DSS, Dr. Peter Afunanya, ya tabbatar da cewa jami'ansu suna kokarin shawo kan lamurran domin bai wa 'yan Najeriya kariya.

Takardar wacce jaridar Vanguard ta gani a ranar Litinin, ta lissafa jihohin da masu son tada tarzomar suka mayar da hankali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel