Magidanci ya bayyana kiyayyar da ke tsakanin mahaifiyarsa da matarsa na shekaru 7

Magidanci ya bayyana kiyayyar da ke tsakanin mahaifiyarsa da matarsa na shekaru 7

- Wani mutum ya yi wata wallafa ta shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter wacce ta janyo cece-kuce

- Mutumin ya bayyana yadda yake zaune da matarsa na tsawon shekaru 7 amma mahaifiyarsa bata son ta

- Duk da dai bai bayyana dalilan da suka sanya mahaifiyarsa tsanar matar tasa ba, amma ya ce ya rungumi kaddararsa

Wani mutum dan Najeriya ya bayyana yadda rayuwar aurensa na shekaru 7 ta kasance tsakanin matarsa da mahaifiyarsa wacce bata kaunarta ko kadan, a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Mutumin ya ce dama can mahaifiyarsa bata son matar da ya aura. Bai sanar da dalilanta na hakan ba, amma ya bayyana yadda ya amince da kaddararsa, ya cigaba da zama da matarsa na shekaru 7.

Kamar yadda ya wallafa, "Shekaru 7 kenan ina zaune da matata, amma mahaifiyata bata son ta. Tuni na amince da kaddarata na cigaba da rayuwa a haka."

Magidanci ya bayyana kiyayyar da ke tsakanin mahaifiyarsa da matarsa na shekaru 7
Magidanci ya bayyana kiyayyar da ke tsakanin mahaifiyarsa da matarsa na shekaru 7. Hoto daga @iAmSeunKentebe
Asali: Twitter

KU KARANTA: Allah ya yi wa tsohon gwamnan Kano, Isah Kontagora, rasuwa

A wata wallafa da yayi bayan wannan, ya ce bai yi tunanin wallafarsa za ta yadu ba. Ya ce mahaifiyarsa tana da kirki, kawai dai jininta bai hadu da na matarsa bane, kuma ta riga ta kwallafa rai akansa, da yake shine dan ta na farko.

Kamar yadda ya wallafa, "Na kara wannan wallafar ne don kada a yi ta caccakar mahaifiyata. Na fahimci cewa iyaye da dama basa iya hakura da dansu na farko, dalilin haka mata suke ganin kamar zakewa ce. Zan yi ta hakuri da mahaifiyata har sai ta hakura."

KU KARANTA: 'Yar bautar kasa ta sha duka, an yi mata tumbur bayan kashe saurayin da ta kwana da shi (Hotuna)

Bayan wannan wallafar ne mutane suka yita cece-kuce iri-iri, har suke ganin cewa mahaifiyarsa bata kyauta ba, idan za a tsani mutum, ya kamata a samo kwararan hujjojin yin hakan.

A wani labari na daban, direbobin tifa a ranar Lahadi sun rufe babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto bayan zargin kama mambobinsu da jami'an tsaro suke yi, TVC News ta wallafa hakan.

Wannan matakin da direbobin tifan suka dauka ya tsayar da motoci masu kaiwa da kawowa a Gada biyu na fiye da sa'o'i biyu a babbar hanyar.

Kungiyar na zargin jami'an NSCDC da cutar dasu matuka na kusan watanni shida.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel