Sarkin Billiri, Dr Abdu Buba Maisheru II (Mai Tangale) ya mutu

Sarkin Billiri, Dr Abdu Buba Maisheru II (Mai Tangale) ya mutu

- Allah ya yi wa tsohon gwamnan Gombe kuma Sarkin Billiri Dr Abdu Buba rasuwa

- Tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Dankwambo ya yi wa iyalan Sarkin da al'ummar jihar ta'aziyya

- Ɗankwambo ya ce rasuwar Sarkin babban rashi ne ya kuma yi addu'ar Allah ya gafarta masa

Tsohon gwamnan Jihar Gombe, kuma jigo a jam'iyyar Peoples Democratic Party, ya sanar da rasuwar Sarkin mai daraja ta farko cikin wani sako da ya wallafa a Twitter.

Dankwambo ya yi wa iyalan Sarkin da al'ummar Jihar ta'aziyya game da rasuwar Sarkin.

Sarkin Billiri, Dr Abdu Buba Maisheru II (Mai Tangale) ya mutu
Sarkin Billiri, Dr Abdu Buba Maisheru II (Mai Tangale) ya mutu. Hoto: @HEDankwambo
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kai wa Sanata hari a Osun yayin taro a mazaɓarsa

Ya rubuta;

"Ni da iyalaina na son miƙa sakon ta'aziyyar mu ga mutanen Gombe game da rasuwar Mai Martaba, Dr. Abdu Buba Maisheru II (Mai Tangale) Sarkin Billiri. Rasuwarsa ya zo mana a matsayin abun mai firgici amma muna addu'ar Allah ya jiƙansa,"

KU KARANTA: Korona ta yi ajalin likitan Fafaroma Francis

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel