Boko Haram: An kona makaranta da dakin jinya a Garin Gujba, Jihar Yobe

Boko Haram: An kona makaranta da dakin jinya a Garin Gujba, Jihar Yobe

-Ana zargin ‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari a garin Gujba, Yobe

-Dakarun Najeriya sunyi namijin kokari, sun fatattaki Sojojin ‘Yan ta’adda

-Kafin yanzu an kai hari a karamar hukumar Geidam, har an sace wani Basarake

Wasu ‘yan ta’addan da ake zargin cewa ‘yan kungiyar nan ta Boko Haram ne sun kai hari a garin Gujba, jihar Yobe, sun shiga harbin Bayin Allah.

Wannan hari da aka kai a ranar Asabar, 9 ga watan Junairu, 2020, ya zo ne sa'o'i bayan jami’an tsaro sun kaddamar da shirin Tura Ta Kai Bango.

Wani mazaunin garin Gujba yayi magana da jaridar Punch jiya, ya tabbatar da cewa an kai masu hari, sun ji karan bindigogi, dole suka tserewa ransu.

Majiyar ta shaidawa manema labarai cewa ‘yan ta’addan sun kona wani wurin jinyar marasa lafiya da makaranta da muhimman gina-gine a garin.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mutane, sun tsere da dabbobi a Zamfara

“’Yan Boko Haram sun duro garinmu da kimanin karfe 2:30 na rana, suka shiga harbe-harbe, wannan ya sa mutanenmu suka tsere.” Inji majiyar.

Ya kuma ce: “Suka rusa makarantar firamare da wasu kayan aikin gine-ginen da ake yi a garin.”

Mazaunan wannan gari sun bayyanawa manema labarai cewa kafin a kai wannan hari, sai da ‘yan ta’addan suka bada sanarwar zuwansu a wata wasika.

Jama’an wannan yanki na Gujba sun yaba da kokarin sojoji da suka tare hanyar Katarko, suka hana ‘yan ta’addan shiga cikin gari domin kai wani harin.

KU KARANTA: An tarwatsa mafakar 'Yan bindiga a Jihar Kaduna

Boko Haram: An kona makaranta da dakin jinya a Garin Gujba, Jihar Yobe
Gwamnan Jihar Yobe, Mala Buni Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: UGC

Dakarun sojoji sun budawa ‘yan ta’addan wuta, wannan ya yi sanadiyyar fatattakan ‘yan ta’addan da suka addabi yankin na Arewa maso gabashin Najeriya.

A makon jiya kun ji ‘yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a karamar hukumar Geidam. An sace Hakimin Maganna a karkashin masarautar Ngazargamu.

‘Yan ta’addan na Boko Haram sun kona gidaje da shaguna bayan sun saci kayan abinci.

Nai girma gwamna Mai Mala Buni ya fito ya yi magana, ya bada umarni ga ma’aikatan bada agajin gaggawa na SEMA, su kai doki zuwa garin na Geidam.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel