Dangote, Isyaka Rabiu, da wasu attajirai biyu ne biloniyoyin Najeriya 4 a 2020, Forbes
- A bisa rahoton Forbes na 2020, mutane 4 kacal suka samu shiga jerin biloniyoyin nahiyar Afrika
- Wadannan attajirai sun samo arzikinsu ne daga mana'antu da rijiyoyin man fetur
- Daga cikin mutanen 4, Aliko Dangote ne bakin mutum mafi arziki a duniya kuma dan Najeriya mafi daula
Yayinda Najeriya ke alfahari da manyan attajirai kuma masu hannun da shuni, yan kalilan ne kadai suka kai matsayin buloniyoyi bisa rahoton mujallar Forbes.
Yan Najeriya hudu kadai cikin masu kudin Najeriya suka samu shiga jerin buloniyoyin duniya kuma sune Aliko Dangote, Mike Adenuga, Folorunsho Alakija, da Abdulsamad Isyaka Rabiu.
Ga jerin yan Najeriya hudu da suka samu shiga:
1. Aliko Dangote - $10.1bn (N3,850,120,000,000)
Dangote, har ila yau ya kasance bakin mutum mafi arziki a fadin duniya. Ya samo arzikinsa ne daga masana'antu daban-daband a ya mallaka irinsu Taliya, Sukari, Gishiri da Siminti.
Yanzu haka yana gina matatar mai wacce za ta shiga jerin mafi girma a duniya.
2. Mike Adenuga - $7.7bn (N2,935,240,000,000)
Adenuga, wanda shine mamallakin kamfanin sadarwan Glo ne na biyu a jerin attajiran nahiyar Afirka.
KU DUBA: Ranar 3 ga Disamba zamu kammala aiki kan kasafin kudin 2021, Majalisar dattawa
3. Abdulsamad Rabiu - $3.13bn (N1,193,156,000,000)
Shugaban kamfanin BUA ne na uku a Najeriya amma na takwas a nahiyar. Ya samo arzikinsa a masana'atu irinsu Siminti, Sukari, gine-gine.
Dan asalin jihar Kano ne kuma yana da shekara 60 a duniya.
4. Folorunsho Alakija - $1bn (N381,200,000,000)
Ita ce mutum na 20 a jerin attajiran duniya kuma ta hudu a Najeriya. Ta samo arzikinta ta kamfanin mai Famfa Oil.
KARANTA: An haifi yaro da mazakuta biyu a babban asibitin yara dake kasar Masar
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng