Tarihin kasuwanci da rayuwar ‘Dan kasuwan Duniya Aliko Dangote

Tarihin kasuwanci da rayuwar ‘Dan kasuwan Duniya Aliko Dangote

Yanzu haka dai Attajirin Nahiyar Afrika Aliko Dangote ya haura shekaru 60 bayan da jiya yayi bikin cika shekaru 61 da haihuwa. Dangote ya taba zama na 23 a jerin Attajiran Duniya. Yanzu haka dai ya mallaki sama da Biliyan Dala 14.1.

Tarihin kasuwanci da rayuwar ‘Dan kasuwan Duniya Aliko Dangote
Babban Attajirin Duniya Aliko Dangote ya cika shekara 61

Ya kamata jama’a su san shin wai wanene Dangote don haka mu ka tsakura kadan daga cikin tarihin sa:

1. Dangi da Nasaba

An haifi Aliko Dangote ne cikin Dangin Attajirin nan watau Alhaji Alhassan Dantata. Mahaifiyar Dangote Hajiya Mariya Sanusi ‘Diya ce wajen tsohon mai kudin Yankin na Afrika.

2. Kuruciya

‘Dangote yayi karatun kasuwanci ne a Kano da kuma wata Jami’a da ke cikin Birnin Misra watau Masar. Tun Dangote yana yaro yake saida alewa har ya girma ya samu daukaka.

KU KARANTA: Ko ka san su wanene manyan masu kudin Najeriya

3. Kasuwanci

A shekarar 1977, Aliko Dangote ya fara shiga harkar kasuwanci da kyau bayan ya bude kamfanin sa a Legas. Yanzu dai duk Afrika Dangote bai da tamka a maganar neman kudi.

4. Siyasa

Aliko ‘Dangote yana cikin wadanda su ka ba Cif Olusegun Obasanjo gudumuwar yakin neman zabe a 1999 kuma wasu na ganin Gwamnati na yi da shi duk da bai da sha’awar fitowa takara.

5. Rayuwa

A tarihi Aliko Dangote ya auri mata akalla 4 a lokaci daban-daban wanda kusan duk su ka rabu inji marubuta, ana kuma tunanin cewa ya hafi ‘Ya ‘ya 15, sai dai kusan yaran sa mata 3 ne aka fi sani a Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng