Dangote, da sauran manyan mutane 7 da suka fi kowa arziki a Afirka
- A rahoton da Africa Facts Zone ta fitar, ya nuna cewa, Aliko Dangote shi ne mahalukin da ya fi kowane mutum kudi a nahiyar Afirka, yayin da dukiyar da ya mallaka ta kai dala biliyan 9.5.
- Mutum na biyu da ya fi kowa arziki a Afirka, shi ne Nicky Oppenheimer, wanda ya fito daga Afirka ta Kudu kuma ya mallaki dukiya da darajarta ta kai dala biliyan 7.5 (N2,902,500,000,000)
- Cikin jerin mutane takwas da suka fi kowa dukumar dukiya a nahiyyar Afirka, Najeriya ta na da attajirai uku da suka hadar da Mike Adenuga da Abdussamad Rabi'u wanda ke zaman na hudu da na takwas a jerin
A sha'ani na kasuwanci ko siyasar duniya, samun dukiya yana da matukar muhimmanci. Mujallar Africa Facts Zone ta wallafa jerin manyan mutane 8 mafi arziki a nahiyar Afirka.
Aliko Dangote, ya ja ragamar duk wani attajiri a nahiyar Afirka, yayin da dukiyar da ya mallaka ta kai dala biliyan 9.5.
Wannan adadi na dukiya da Dangote ya mallaka wadda ta sa ya kere kowa arziki, shi ne kwatan kwacin tiriliyan hudu ba kadan a kudin Najeriya (N3,676,500,000,000).
Dan kasar Afirka ta Kudu, Nicky Oppenheimer, shi ne ya biyo bayan Dangote da tarin dukiya wadda ta kai dala biliyan 7.5, Naira 2,902,500,000,000 kenan a kudin Najeriya.
Mutum na biyu da ya fi kowa arziki a Afirka, Nicky Oppenheimer, ya fito ne daga kasar Afirka ta Kudu kuma ya mallaki dukiya da darajarta ta kai dala biliyan 7.5 (N2,902,500,000,000)
Wani dan Najeriyar da ya shiga cikin jerin attajiran takwas shi ne Mike Adenuga, wanda ya mallaki dukiyar da ta kai dala biliyan 5.8, Naira 2,244,600,000,000 kenan.
Abdussamad Rabi'u, shi ne dan Najeriya na uku da ya shiga cikin jeranton yayin da ya mallaki dukiya ta dala biliyan 3.2 (N1,238,400,000,000).
1. Aliko Dangote - $9.5bn (N3,676,500,000,000)
Aliko Dangote wanda ya shekar 63 a duniya kuma haifaffen jihar Kano, ya mallaki dala biliyan 9.5 (3,67,500,000,000). Shi ne mamallaki kuma shugaban gidauniyar Dangote.
2. Nicky Oppenheimer - $7.5bn (N2,902,500,000,000)
Nicky Oppenheimer, dan kasar Afrika ta Kudu, ya mallaki kimanin dala biliyan bakwai da rabi. Kwatan kwacin Naira 2,902,500,000,000,000 a kudin Najeriya.
Shine tsohon shugaban kamfanin hako ma'adanin lu'u-lu'u na De Beers, kuma tsohon mataimakin shugaban kamfanin hako ma'adanai na Anglo American.
3. Naseef Sawiris - $6.3bn (N2,438,100,000,000)
Sawiris wanda aka haifa a shekarar 1961, yana daya daga cikin zuri'ar dangin da ya fi kowanne arziki a kasar Masar. Tun daga shekarar 1982, Sawari ya rike manyan mukamai a wasu shahararrun kungiyoyi na duniya daban daban masu tarin yawa.
4. Mike Adenuga - $5.8bn (N2,244,600,000,000)
Adenuga, hamshakin mai kudi a Najeriya da ya shahara a kan kasuwancin sadarwar ta fasahar zamani, shi ne shugaban kamfanin sadarwa na Globacom.
Kamfanin sadarwa na Globacom wanda aka fi sani da Glo, ya shahara a wasu kasashen Afrika kamar Najeriya da Benin.
KARANTA KUMA: Buhari da Trump ba su damu da al'ummar su ba - Wizkid
5. Johann Rupert - $4.9bn (N1,896,300,000,000)
Johann Peter Rupert, dan kasar Afrika ta Kudu ne kuma shi ne babban dan hamshakin dan kasuwar nan, Anton Rupert.
Johann ya yi nisa a harkar kasuwancin kayayyaki na alfarma, kuma shi ne mai kamfanin Compagnie Financière Richemont SA.
6. Issad Rebrab - $4.5bn (N1,741,500,000,000)
Issad Rebrab, gogarman dan kasuwa ne a kasar Algeria kuma ana ikirarin shi ne shugaban mafi girman kamfanin 'yan kasuwa masu zaman kansu na Cevital industrial group.
7. Mohammed Mansour - $3.3bn (N1,277,100,000,000)
Mohammed Mansour, dan kasuwa ne a kasar Masar kuma tsohon dan siyasa. Shi ne shugaban gidauniyar Mansour. Kamfaninsa shi ne na biyu mafi girma a kasar Masar ta fuskar samun kudaden shiga.
8. Abdulsamad Rabiu - $3.2bn (N1,238,400,000,000)
Dan Marigayi Sheikh Isiyaka Rabi'u, shi ne shugaban kamfonin BUA, wanda ake samar da siminti, sukari, kayayyakin abinci da kuma harkar gidaje, filaye da gonaki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng