ASUU ta hadu a kan “Babu tanadin da aka yi domin maganin cutar COVID-19”

ASUU ta hadu a kan “Babu tanadin da aka yi domin maganin cutar COVID-19”

-Malaman Jami’a basu goyon bayan a bude wuraran karatu a halin da ake ciki

-ASUU tana ganin cewa ba a shiryawa yaki da annobar COVID-19 a jami’o’in ba

-Shugabannin kungiyar ASUU duk sunyi tarayya a kan hadarin bude aji yanzu

Bangarorin kungiyar malaman jami’a a Najeriya sun duba halin da ake ciki game da annobar COVID-19, sun ce bai dace a bude makarantu ba.

Jaridar Punch ta fitar da dogon rahoto a ranar Lahadi wanda ya nuna malaman jami’o’i da-dama basu goyon bayan a koma karatu a ranar 18 ga wata.

ASUU tace ta shirya komawa aiki, amma gwamnati ba ta yi tanadin da ake bukata domin kare ma’aikata da dalibai daga kamuwa da COVID-19 ba.

Shugaban ASUU na jami’ar Obafemi Awolowo, Osun, Dr. Adeola Egbedokun yace dakunan kwana da na karatu sun saba sharudan yaki da annobar.

KU KARANTA: Akwai yiyuwar barkewar sabon yajin aiki a Jami'o'i

Haka zalika kungiyar ASUU ta jami’ar aikin gona ta tarayya da ke garin Abekoya, ta ce ba za ta iya tunkarar kalubalen annobar cutar Coronavirus ba.

Shugaban ASUU na jami’ar FUNAAB, Dr. Adebayo Oni ya yi hira da Punch, yace dakunansu a cike suke makil, kuma babu wuraren wanke hannuwa.

Malaman jami’an ATBU ta bakin shugaban ASUU na makarantar, Dr. Musa Babayo, yana kan wannan ra’ayi, yace hukumomi ba suyi wani tanadi ba.

Babayo yake cewa da aka tafi yajin aiki makarantu da gwamnati ba suyi wani kokarin ganin yadda za a tunkari annobar a dakunan aji da karatu ba.

KU KARANTA: Shugabannin ASUU sun yi zama domin duba yiwuwar bude Jami’o’i

ASUU ta hadu a kan “babu tanadin da aka yi domin maganin cutar COVID-19”
Jami'ar Jos Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

ASUU ta reshen jami’ar UNIJOS, tana tsoron halin da ake ciki. Shugaban kungiyar, Dr. Lazarus Maigoro yace babu shakka cutar COVID-19 ta sake barkowa.

Shugabannin ASUU na jami’o’in Calabar da Fatakwal, Dr John Edor da Dr Austen Sado, basu goyon bayan a jefa malamai cikin hadari da komawa bakin karatu.

A makon da ya gabata mun tattaro maku jerin sunayen manyan jami’o’in Najeriya da suka sanar da ranar komawa makaranta kawo yanzu a fadin kasar nan.

Jami'o'in Bayero da ke Kano, da UNIBEN da ke jihar Edo, da kuma jami'ar tarayya ta Ilorin duk sun yi alkawarin zasu koma bakin aiki a cikin watan Janairu.

Ita dai gwamnatin tarayya ta bakin hukumar NUC umurci jami’o’in kasar su fara shirin komawa aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel