Jerin sunayen jami’o’in Najeriya da suka sanar da ranar komawa makaranta

Jerin sunayen jami’o’in Najeriya da suka sanar da ranar komawa makaranta

- Bayan kimanin watanni tara da jami'oin Najeriya suka dauka a rufe saboda yajin aikin da kungiyar malaman ASUU suka tafi wasu makarantu sun sanar da ranar dawowa

- Jami'o'in BUK, UNIBEN da Uni Ilorin duk za su koma bakin aiki a wannan wata ta Janairu

- Sai dai ga dukkan alamu za a dunga koyar da dalibai ne ta yanar gizo kamar yadda hukumar NUC ta umurta don yaki da yaduwar annobar korona

Daga karshen watan Maris zuwa Disamban 2020, jami’o’in gwamnati na Najeriya sun rufe saboda yajin aikin da kungiyar malaman ASUU suka tafi.

Bayan tsawon watanni da aka kwashe ana tattaunawa, daga karshe kungiyar malaman sun dakatar da yajin aiki a ranar Laraba, 23 ga watan Disamba.

Sai dai kuma, makarantu basu koma karatu nan take ba saboda dama kasar ta shiga lokaci na bukukuwa wanda ke cike da hutu.

Jerin sunayen jami’o’in Najeriya da suka sanar da ranar komawa makaranta
Jerin sunayen jami’o’in Najeriya da suka sanar da ranar komawa makaranta Hoto: Twitter/@unilorinnews, Daily Trust
Asali: UGC

Hakazalika, gwamnatin tarayya ta umurci dukkanin jami’o’in kasar su dakatar da darusa sakamakon yaduwar annobar COVID-19.

KU KARANTA KUMA: 2023: Jigon APC Girei ya ba jam’iyya mai mulki shawarar ba Osinbaj-Zulum tikiti

Hukumar makarantun jami’o’i ta kasa (NUC) ce ta fitar da sanarwar a wata wasika dauke da sa hannun mataimakin babban sakatarenta, Chris Maiyaki.

Sai dai, wasu jami’o’in sun sanar da ranakun komawarsu a yanzu. Legit.ng ta tattara jerin jami’o’in gwamnati da ke shirin komawa ajujuwa a watan Janairu.

1. Jami’ar Ilorin

Hukumar jami’ar Ilorin ta kaddamar da cewa makarantar za ta koma bakin aiki gadan-gadan a ranar 11 ga watan Janairun 2021.

Jami’ar ta yi bayanin cewa za a dunga koyar da darasi ne ta yanar gizo daidai da umurnin hukumar NUC.

2. Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK)

Hukumar gudanarwa ta jami'ar Bayero da ke Kano ta amince da soke zangon karatu na 2019/2020 da aka fara a dukkan fadin makarantar.

Kamar yadda hukumar ta bayyana, dalibai masu digirin farko, za su fara zangon karatunsu ne a ranar 18 ga watan Janairu yayin da sashi na biyu na zangon karatunsu zai fara a ranar 3 ga watan Mayun 2021.

Ga masu digiri na biyu da na uku, hukumar gudanarwar ta bayyana ranar 18 ga watan Janairu da zama ranar farko ta sashin karatu na farko inda sashi na biyu zai fara a 1 ga watan Yuni.

KU KARANTA KUMA: Tattaunawa kan Buhari ba alheri bane ga kwakwalwa ta, in ji Soyinka

3. Jami’ar Benin (UNIBEN)

Hukumar makaranta ta kuma umurci dukkanin dalibai (tsoffi da sabbi) na jami’ar Benin (UNIBEN), jihar Edo, dasu dawo zangon karatu na 2019/2020 da 2020/2021 a ranar 30 ga watan Janairun 2021.

Premium Times ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a na makarantar, Benedicta Ehanire ta fitar a karshen taron hukumar gudanarwa ta jami’ar a ranar Litinin, 4 ga watan Janairu.

A wani labarin, Billionaire din nan na China Jack Ma ba a san inda yake ba tsawon watanni biyu tun lokacin da ya yi wani jawabi mai cike da cece-kuce a kan gwamnatin Xi Jinping.

Attajirin attajirin nan kuma wanda ya kirkiro kamfanin Alibaba ya zargi Jam’iyyar Kwaminis ta Tsakiya (CCP) da dakile kirkire-kirkire.

Attajirin dan kasuwar ya kirayi masu kula da harkokin kudi na gwamnati da kuma bankunan mallakin gwamnati inda ya kamanta su da 'tsohuwar kungiyar kulob din' da ke kokarin kawo gyara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng