Tsohon shugaban sojin saman Najeriya, Nsikak Edouk, ya rasu
- Gwamnatin Akwa Ibom ta sanar da mutuwar tsohon shugaban sojin sama, Nsikak Eduok
- Ya rasu a Uyo yayin da yake da shekaru 73 a duniya bayan fama da yayi da ciwon koda
- Gwamnatin jihar ta kwatanta shi da dattijo wanda ya bada gudumawar cigaba ga kasar
Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta sanar da rasuwar tsohon shugaban sojin sama, Air Marshal Nsikak Eduok, Daily Trust ta wallafa.
Eduok tsohon shugaban ma'aikatan sama ne kuma ministan sufurin jiragen sama kuma mutuwarsa tana zuwa ne bayan kwwanaki kadan da rasuwar Air Commodore Nkanga mai ritaya.
Kamar yadda takardar ta fito sanye da hannun sakataren gwamnatin jihar, Dr Emmanuel Ekuwem a ranar Alhamis, Eduok ya rasu a ranar Laraba, 6 ga watan Janairun 2021 bayan fama da ciwon koda da yayi.
KU KARANTA: Bidiyon Kakan da ya kai jikonkinsa gwajin DNA, ya gano ba shi ya haifa mahaifinsu ba
An kwantanta Eduok da dattijon da za a yi matukar kewarsa sakamakon ayyukan cigaba da ya samarwa jiharsa da kasar baki daya.
"Gwamnatin jihar Akwa Ibom tana sanar da mutuwar tsohon shugaban ma'aikatan sama sakamakon ciwon koda da yayi fama da ita.
"Ya rasu a ranar 6 ga watan Janairun 2021 a garin Uyo. Bayanai daga likitoci ya bayyana cewa ciwon koda ce ta yi ajalinsa.
"Dattijon ya kasance wanda ake matukar mutuntawa a Najeriya da Akwa Ibom saboda rawar da ya taka wurin kawo cigaba da jiharsa da kasa baki daya," yace.
Eduok ya rasu yana da shekaru 73 a duniya kuma shine shugaban sojin sama na 12 wanda yayi murabus a 1999.
KU KARANTA: Fitattun mutane10 da rasuwarsu ta matukar girgiza jihar Katsina a 2020
A wani labari na daban, annobar korona ta yi mummunar illa ga tattalin arzikin jihohi da dama na Najeriya ballantana jihar Kano.
Hakan yasa gwamnatin jihar Kano ta sanar da komawa biyan ma'aikatanta karancin albashin N18,000 a maimakon N30,000 da ta fara bayan boren da kungiyar kwadago tayi, The Cable ta ruwaito.
A yayin tabbatar da wannan cigaban, mai magana da yawun Gwamna Umaru Ganduje, Salihu Tanko-Yakasai, ya ce halin da kasar nan ta shiga sakamakon annobar korona ce ta saka hakan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng