Bidiyon 'yar majalisa matar aure ɗare-ɗare a cinyar dan majalisa ya janyo cece-kuce

Bidiyon 'yar majalisa matar aure ɗare-ɗare a cinyar dan majalisa ya janyo cece-kuce

- Cece-kuce ya barke bayan yaduwar bidiyon wata 'yar majalisar Ghana, wacce matar aure ce zaune a cinyar wani dan majalisa

- Hakan ya janyo surutai kala-kala, bayan nan ne rikici ya barke tsakanin 'yan majalisar dake karkashin NPP da NDC

- Wannan lamari ya daure wa kowa kai har ta kai ga an gayyaci dan majalisar da aka ga abokiyar aikinsa ɗare-ɗare a cinyarsa don jin ta bakinsa

Wani al'amari mai ban mamaki ya faru yayin da wasu 'yan majalisar Ghana suka kwashi damben naushi.

Al'amarin ya faru ne bayan wata 'yar majalisa ta zauna ɗare-ɗare akan cinyar abokin aikinta a cikin majalisa, The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda bidiyon yayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, an tattaro bayanai akan yadda rigima ta kwabe tsakanin 'yan jam'iyyar NPP da na NDC wanda hakan sanadiyyar rabuwar kai ne akan wanda zai tsaya matsayin kakakin majalisar.

Bidiyon 'yar majalisa ɗare-ɗare a cinyar dan majalisa ya janyo cece-kuce
Bidiyon 'yar majalisa ɗare-ɗare a cinyar dan majalisa ya janyo cece-kuce. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hukuncin kuskure: Za a biya wani mutum N3.7bn bayan kwashe shekaru 28 a gidan kurkuku

An gano cewa NPP ce jam'iyya mai rinjaye, wacce take da kujeru 137, yayin da NDC take da kujeru 136.

Sai da sojoji suka je har majalisar tukunna suka sasanta komai.

An ga 'yar majalisar wacce matar aure ce, Ursula Owusu-Ekuful, a zaune a cinyar wani dan majalisar kafin fadan ya barke tsakanin 'yan majalisar dake karkashin NPP da na NDC akan wadanda za su samar da kakakin majalisar.

A wata tattaunawa da Joy News suka yi da dan majalisar, Kwabena Mintah Akandoh, wanda aka ga Ursula zaune ɗare-ɗare akan cinyarsa, inda yace "Yayin da 'yan jam'iyyar NPP suka shiga majalisar, sun gan mu zaune a bangaren dama, sai suka koma bangaren hagu amma Ursula ta ki zuwa.

"Cletus Avoka yana zaune sai ya mike don yaje bandaki, lokacin da ya dawo Ursula ta zauna a wurinsa. Mun yi kokarin jan ra'ayinta kawai sai ta zauna a cinyata ba tare da ta ce min komai ba."

KU KARANTA: Ganduje zai koma biyan N18,000 karancin albashi, ya bayyana dalilinsa

A wani labari na daban, bude iyakokin tudun kasar nan hudu da gwamnatin tarayya tayi a makon da ya gabata ya taka rawar gani wurin ragargaza farashin hatsi da sauran kayan abinci.

Hakazalika hakan ya dakatar da al'amura masu tarin yawa a kasuwanni jihar Katsina, Katsina Post ta wallafa.

Kafin sanar da bude iyakokin tudun, 'yan kasuwar hatsi da wasu 'yan kasuwa suna boyewa da sunan wakilan kamfanoni inda suke siyan kayan gona da yawa kuma suke boyewa domin samun riba a nan gaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel