Nasara daga Allah: Bidiyon sojin sama suna ragargaza shugabannin Boko Haram

Nasara daga Allah: Bidiyon sojin sama suna ragargaza shugabannin Boko Haram

- Rundunar sojin Operation Lafiya Dole ta yi raga-raga da manyan shugabannin Boko Haram

- Ta jiragen yaki dakarun suka yi wa Alagarno ruwan wuta, yankin da shugabannin 'yan ta'addan ke zama

- Suna samun damar kitsa makirci tare da zama a wurin sakamakon bishiyoyin da suka yawaita a yankin

Rundunar sojin sama ta Operation Lafiya Dole ta yi wa 'yan ta'addan Boko Haram mummunar barna a dajin Sambisa da ke jihar Borno.

Ta ragargaza maboyar wasu manyan shugabannin 'yan ta'addan da ke Alagarno wanda aka gano shugabannin ne kadai ke zama a wurin.

Wurin na boye a kasan bishiyoyi kuma yana da nisan kilomita 2.3 arewa maso gabas daga KAFA, inda 'yan ta'addan ke amfani da shi wurin shirya makircinsu.

Bidiyon ruwan wuta da sojin sama suka yi a Sambisa, sun sheke 'yan ta'adda masu yawa
Bidiyon ruwan wuta da sojin sama suka yi a Sambisa, sun sheke 'yan ta'adda masu yawa. Hoto daga @DafenceInfoHQ
Asali: UGC

Kamar yadda Manjo Janar John Enenche ya fitar a wata takarda ranar Alhamis, 7 ga watan Janairun 2021, an samu wannan nasarar ne bayan ruwan wutar da aka yi wa yankin.

Da farko sojin sama sun samo bayani a kan daidai inda 'yan ta'addan suke kafin su yi amfani da jiragen yaki wurin ragargazarsu daga rana har zuwa dare.

Rundunar sojin Najeriyan ta tabbatar da cewa ba za ta sassauta ba wurin kawo karshen makiyan kasar nan tare da kawo zaman lafiya da tsaro a dukkan yankuna.

KU KARANTA: Kutse a majalisa: Rayuka 4 sun salwanta, an damke magoya bayan Trump masu yawa

KU KARANTA: Kasafin kudin 2021: N2.42bn na tafiye-tafiye, N135m na lemuka aka warewa fadar Buhari

A wani labari na daban, a wata takarda da kakakin hukumar 'yan sanda, Gambo Isah ya saki, ya tabbatar da yadda 'yan sanda suka kashe 'yan bindiga 6 a jihar Katsina.

'Yan sandan sun kai samame ne a ranar 1 ga watan Janairun 2021, inda suka samu nasarar kwatar miyagun makamai kamar bindigogi kirar G3, AK 47, LAR, bindigogin toka guda biyu da 10 rounds na 7.62mm ammunition a hannunsu.

"A ranar 2/1/2021 sun samu nasarar kwatar AK 47 da 32 rounds na 7.62mm ammunition a Pauwa Bushland dake karamar hukumar Kankara dake jihar Katsina," a cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel