Rahama Sadau ta gana da kwamishinan fina-finai na Quebec a kasar Canada

Rahama Sadau ta gana da kwamishinan fina-finai na Quebec a kasar Canada

- Rahama Sadau ta gana da kwamishinan fina-finai na Quebec, kasar Canada amma a Dubai

- Jarumar ta sanar da hakan a wata wallafa da tayi a shafinta na Instagram tare da hotonsu

- Ta sanar da cewa sun tattaunawa a kan yuwuwar fim din hadin guiwa tare da su

Jaruma Rahama Sadau ta samu damar ganawa da kwamishinan fina-finai na Quebec da ke kasar Canada.

Kamar yadda jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram, ta sanar da cewa ta samu ganawa da Hans Fraikin a yayin da ta kai ziyara daular larabawa.

Kamar yadda ta wallafa, "Dole ne in ce 2021 ta fara da farin ciki. A yayin hutu na, shakawata da abokai, ziyara da sauransu da nayi a UAE, na samu damar ganawa da Hans Fraikin, kwamishinan fina-finai na Quebec ta kasar Canada."

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Bidiyon sojin sama suna ragargaza shugabannin Boko Haram

Rahama Sadau ta gana da kwamishinan fina-finai na Quebec a kasar Canada
Rahama Sadau ta gana da kwamishinan fina-finai na Quebec a kasar Canada. Hoto daga Rahamasadau
Asali: Instagram

Kamar dai yadda aka gano, Fraikin shine mashiryin manyan fina-finai masu dogon zango da suka hada da Mission impossible- Fallout, 6 Underground, Fast & Furious 7, Bang Bang, Tiger Zinda Hain da the list goes on.

Idan dai za mu tuna, an fatattaki jarumar daga masana'antar fina-finan hausa sakamakon wasu laifuka da ta aikata.

KU KARANTA: Matashi ya bayyana yadda budurwarsa ta rabu da shi saboda ya ki fara 'Yahoo'

A wani labari na daban, wani al'amari mai ban mamaki ya faru yayin da wasu 'yan majalisar Ghana suka kwashi damben naushi.

Al'amarin ya faru ne bayan wata 'yar majalisa ta zauna ɗare-ɗare akan cinyar abokin aikinta a cikin majalisa, The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda bidiyon yayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, an tattaro bayanai akan yadda rigima ta kwabe tsakanin 'yan jam'iyyar NPP da na NDC wanda hakan sanadiyyar rabuwar kai ne akan wanda zai tsaya matsayin kakakin majalisar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel