Tagwaye sun auri miji ɗaya saboda baza su iya rabuwa da juna ba (Bidiyo da Hotuna)

Tagwaye sun auri miji ɗaya saboda baza su iya rabuwa da juna ba (Bidiyo da Hotuna)

- Wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna bikin wasu tagwaye

- A cewar wani mai amfani da shafin Twitter da ya wallafa labarin, ya ce yan uwan sun auri mutum guda ne

- Dalilin auren mutum daya shi ne baza su iya rayuwa ba tare da juna ba

Ana iya jin labarin tagwaye da suka shaku da juna har ta kai baza a iya raba su ba, amma ba a saba jin su auri mutum daya saboda wannan dalili ba.

To, wannan ne ya faru da wasu tagwaye da suka auri miji daya saboda basa son rabuwa.

Tagwaye sun auri miji ɗaya saboda baza su iya rabuwa da juna ba (Bidiyo da Hotuna)
Tagwaye sun auri miji ɗaya saboda baza su iya rabuwa da juna ba (Bidiyo da Hotuna). Hoto: @Ph_Obidon
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Abinda yasa aka canja na a 'Kwana Casa'in', Safiyya

Hotuna bidiyo na auren su na gargajiya sun fito ne daga Nelson Obidon da ya wallafa a shafin Twitter.

Kamar yadda ya shaida, tagwayen sun auri mutum daya ne.

Sun yi shiga cikin kaya irin daya launin ruwan da ruwan zinare irin na aure, an dauki hoton ma'aurata ukun a hoto tare.

Duk da cewa ba a ga wani murmushi a fuskar su ba, amaren sun yi rawa tare kuma an lika musu kudi.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mutum 20 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi

A bidiyon, ana iya ganin daya daga cikin tagwayen da juna biyu, idan har za a binciki tudun ciki da ke kasar rigar ta.

Angon na su ya bayyana cikin tabarau yana farin ciki da kan sa.

Kalli hotona da bidiyo a kasa:

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel