Yanzu-yanzu: Mutum 20 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi

Yanzu-yanzu: Mutum 20 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi

- Mummunan hatsari ya faru tsakanin motar Bas da Golf a Jihar Bauchi

- Fasinjoji 20 cikin 22 da hatsarin ya ritsa da su sun riga mu gidan gaskiya

- Rundunar 'yan sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da afkuwar hatsarin

Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadin rasuwar mutum 20 a Bauchi inda suka kone ta yadda ba za a iya gane su ba.

The Punch ta ruwaito cewa hatsarin wadda ya faru a ranar Lahadi ya ritsa da motocci biyu ne.

An kuma gano cewa mata biyu ne kawai suka tsira da raunika cikin fasinoji 22 da ke cikin motocin biyu.

Yanzu-yanzu: Mutum 20 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi
Yanzu-yanzu: Mutum 20 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da ɗuminsa: Gobara ta tashi a hedkwatar hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya tabbatar da hatsarin a wayar tarho yayin hira da majiyar Legit.ng.

Ya ce hatsarin ya faru ne misalin karfe 3 na rana.

Wakil ya ce, "Eh, hatsarin gaskiya ne kuma ya faru ne a unguwar Tirwun da ke Jihar.

"Hatsarin ya ritsa fasinjoji 22 da ke motocci biyu, Hummer Bus mai wurin zaman mutum 18 na Borno Express da wata mota kirar Golf. Fasinjoji 18 ke cikin Hummar yayinda mutum 4 ke cikin golf din.

"Bus din Borno Express din t fito daga Jos ne tana hanyar zuwa Maiduguri yayin da Golf din ta fito daga Misau ne tana hanyar zuwa Bauchi.

KU KARANTA: Abinda yasa aka canja na a 'Kwana Casa'in', Safiyya

"Da aka sanar da mu, nan take jami'an mu suka garzaya inda abin ya faru don ceto inda suka kai dukkan wadanda abin ya ritsa da su zuwa asibitin koyarwa ta Jami'ar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

"A cikin fasinjojin 22, 20 daga cikinsu sun kone ba a iya gane su yayin da mata biyu sun tsira.

"An ajiye gawarwakin a dakin ajiyar gawa yayin da mutum biyun da suka samu rauni sun karbar magani."

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel