Abinda yasa aka canja ni a 'Kwana Casa'in', Safiyya

Abinda yasa aka canja ni a 'Kwana Casa'in', Safiyya

- Jarumar Kannywood, da ke fitowa a shirin 'Kwana Casa'in', ta sanar da dalilin canja ta da aka yi

- Safiyya ta ce rashin lafiya ne ya kwantar da ita ta gaza zuwa a cigaba da shirin da ita don haka aka maye gurbinta

- Jarumar mai farin jini ta kuma bayyana sabon shirin da ta ke yi mai suna ‘Kaddarar So’

Safiyya Yusuf, jarumar Kannywood wacce ta yi fice saboda rawar da ta taka a cikin sanannen shirin talabijin mai suna ‘Kwana Casa’in’ da ake nuna wa kowanne mako a Arewa 24, Daily Trust ta ruwaito.

Duk da kasancewarta daya daga cikin taurarin shirin da al'umma ke kauna sosai, an cire ta daga shirin ba tare da sanarwa ba. A hirar da ta yi da Weekend Magazine, ta yi karin haske kan hakan da ma wasu abubuwa, ga wani sashi cikin abinda ta fadi.

Abinda yasa aka canja na a 'Kwana Casa'in', Safiiyya
Abinda yasa aka canja na a 'Kwana Casa'in', Safiiyya. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Za a yi jarrabawar 'kimiyyar shanu' ta kasar a India

A cewar Safiyya, "an maye gurbina ne da wata ne a shirin saboda ina ta fama da rashin lafiya sosai a wannan lokacin da ake fim din har ta kai bana iya zuwa wurin aiki"

"An fara daukan sabbin shirin ban samu zuwa ba saboda rashin lafiyar don haka basu da wata zabi ila su maye gurbi na a wannan lokacin."

Jarumar ta fara bayyana cewa ta fito ne a matsayin yarinya wacce ta dage ta yi karatu har da zama likita a shirin.

Mahaifiyarta na fama da matsanancin ciwon kafa don haka ta ke son ta zama likita don ta taimaka mata da ma wasu mutanen.

KU KARANTA: Kotu ta dakatar da Ganduje daga rage albashin ma'aikatan Kano

A bangarensa mahaifinta shi kuma baya son ta da karatun, so kawai yake ta yi aure domin ya samu kudi daga manema auren.

Kazalika, ta ce tana yin wani shirin mai suna ‘Kaddarar So’.

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel