Kotu ta dakatar da Ganduje daga rage albashin ma'aikatan Kano

Kotu ta dakatar da Ganduje daga rage albashin ma'aikatan Kano

- Wata babbar kotun Jihar Kano ta dakatar da gwamna Ganduje daga ragewa ma'aikatan shari'a a jihar albashi

- Shugaban kungiyar JUSUN reshen jihar Kano ya ce idan suka zuba ido za a zabtare sama da miliyan 300 a albashin su kafin

- Alkalin kotun, Usman Naabba ya dage ci gaba da sauraren karar zuwa 28 ga wannan watan

Wata babbar kotun Jihar Kano ta bada wani umarni da ya dakatar da gwamnan jihar da wasu mutane 4 daga sake rage albashin ma'aikatan shari'a a jihar (JUSUN).

Wasu daga cikin mambobin kungiyar ne suka garzaya kotun biyo bayan rage musu albashin watannin Nuwamba da Disamba kusan Naira miliyan 80.

Kotu ta dakatar da Ganduje daga rage albashi
Kotu ta dakatar da Ganduje daga rage albashi. Hoto: @daily_nigerian
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Daga Mali da Sudan ake ɗako hayar yan bindigan da ke adabar arewa, Gwamna Sani-Bello

Karar wanda lauyan su Barista F.I. Umar ya shigar ranar 5 ga Janairu ya kuma kare karar da hujjoji 36

Da ya ke zartar da hukunci, Mai Shari'a Usman Na'abba ya wajabtawa masu kara da duk wanda zai tsaya mu su da ya amince da yarjejeniyar da aka kulla ranar 19 ga Disamba tsakanin bangarorin biyu kafin yanke hukunci na karshe dangane da lamarin.

Ya kuma dage karar zuwa 28 ga Janairu don ci gaba da sauraren karar.

KU KARANTA: 'Yan majalisar Ghana sun bawa hammata iska kan batun rinjaye (Bidiyo)

Da yake zantawa akan batun, shugaban kungiyar JUSUN, Muktar Rabiu Lawal, ya ce sun yi mamakin ganin yanke albashin watannin Nuwamba da Disamba wanda ya samu daukar matakin shari'a.

"A watan Nuwamba an yanke miliyan 41, a Disamba miliyan 39 kuma muka bari aka ci gaba a haka za a zabge fiye da miliyan 300 kafin shekarar nan," a cewar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel