Tambari Yabo, tsohon mataimakin sufeto janar na yan sanda ya mutu

Tambari Yabo, tsohon mataimakin sufeto janar na yan sanda ya mutu

- Najeriya ta yi rashi na Tambari Yabo, wani mataimakin sufeto janar na yan sanda mai ritaya

- Yabo ya mutu a asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo, jihar Sokoto a ranar Asabar, 9 ga watan Janairu

- Sai dai ba a sanar da komai game da rashin lafiyarsa ba

Muhammad Tambari Yabo, mataimakin sufeto-janar na yan sanda mai ritaya, ya mutu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ya mutu a asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo, jihar Sokoto a ranar Asabar, 9 ga watan Janairu, bayan yar gajeriyar rashin lafiya.

KU KARANTA KUMA: FG ta dakatar da diban yan Nigeria 5,000 a hukumar NDLEA

Tambari Yabo, tsohon mataimakin sufeto janar na yan sanda ya mutu
Tambari Yabo, tsohon mataimakin sufeto janar na yan sanda ya mutu Hoto: @aminiyatrust
Asali: Twitter

Koda dai ba a bayyana musababbin ciwonsa ba, Legit.ng ta lura cewa babban jami’in dan sandan mai ritaya ya mutu ne a daidai lokacin da ake sake samun hauhawan wadanda suka mutu sakamakon annobar korona.

An gudanar da jana’izar marigayin da misalin karfe 2.30 na rana, a garin Yabo na Karamar Hukumar Yabo da ke Jihar Sokoto.

Gabanin ya kai mukamin Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda wato AIG, ya rike mukamin Kwamishinan ’Yan Sanda a Kaduna, Kano da Jihar Legas har sau biyu da kuma Oyo da Zamfara da Imo jaridar Aminiya ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Rarara ya gwangwaje jaruman Kannywood da kyautar sabbin motocin alfarma

A wani labari na daban, mun ji cewa kwamishanar lafiyan jihar Kaduna, Hajiya Amina Mohammed Baloni, ta shiga jerin ma'aikatan gwamna El-Rufa'i da suka kamu da muguwar cutar Coronavirus.

Amina Baloni ta bayyana kamuwar da cutar ranar Alhamis, 8 ga Junairu a shafinta na Twitter. Ta bayyana cewa tuni ta killace kanta domin jinya.

Hakazalika ta yi kira ga jama'a su dau wannan cuta da gaske ta hanyar amfani da takunkumin rufe baki, wanke hannu da kuma gujewa taron jama'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel