Da duminsa: Kwamishanar lafiyan jihar Kaduna ta kamu da cutar Korona
- Cutar Korona ta sake waiwaye na biyu, bayan kimanin shekara 1 da bullarta a Najeriya
- A ranar Juma'a, mutane 12 suka rasa rayukansu sakamakon muguwar cutar
- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake Lockdown
Kwamishanar lafiyan jihar Kaduna, Hajiya Amina Mohammed Baloni, ta shiga jerin ma'aikatan gwamna El-Rufa'i da suka kamu da muguwar cutar Coronavirus.
Amina Baloni ta bayyana kamuwar da cutar ranar Alhamis, 8 ga Junairu a shafinta na Twitter.
Ta bayyana cewa tuni ta killace kanta domin jinya.
Hakazalika ta yi kira ga jama'a su dau wannan cuta da gaske ta hanyar amfani da takunkumin rufe baki, wanke hannu da kuma gujewa taron jama'a.
Tace: "Sakamakon sanarwan da na samu cewa na kamu da COVID-19, na shiga killace kaina da kuma jinya."
"Ina kyautata zaton samun waraka da wuri daga wannan cuta."
"Ina kira ga kowa mu dau matakin kare kai da COVID19 irinsu rufe baki, yawan wanke hannu da sabulu da ruwa ko kuma sinadarin tsaftace hannu, da kuma gujewa dandazo."
KU KARANTA: Kwana 3 jere, sama da sabbin mutane 1500 suka kamu da Koronan kullum
KU KARANTA: Zamu kawo karshen Boko Haram da yan bindiga shekarar nan, shugaba Buhari
A bangare guda, gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ya bayyana cewa gaskiya idan adadin sabbin masu kamuwa da cutar Korona ya cigaba da yawa kamar yadda ake samu yanzu, za'a sake kafa dokar hana fita.
Babban jagoran kwamitin yaki da cutar Korona, Dakta Sani Aliyu, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a Abuja, Punch ta ruwaito.
Aliyu yace, "Idan wannan adadin ya cigaba da yawa haka kuma adadin masu mutuwa ya karu, gaskiya babu wata mafita (illa kulle). Idan bamu son a garkame mu, yanzu ne lokacin da ya kamata mubi dokoki."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng