Boko Haram sun kashe mutum 3, sun yi awon gaba da dabbobi a kusa da Maiduguri
- Rayuka uku suka salwanta yayin da wani mutum daya ya samu rauni a sabon harin 'yan Boko Haram
- Mayakan ta'addancin sun kai hari kauyen Ngunari da ke kusa da garin Maiduguri na jihar Borno
- Bayan kashe mutum ukun, sun kwashe akuyoyi, kaji da raguna inda suka yi awon gaba da su
An halaka mutane uku yayin da wani daya ya samu rauni a lokacin da wasu mayakan ta'addanci da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai hari kusa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno a daren Laraba, majiyoyi suka sanar.
An gano cewa 'yan ta'addan sun tsinkayi kauyen Ngunari kusa da Yankin Moromti wurin karfe 10:30 na dare a karamar hukumar Konduga inda suka kashe mutum uku.
Abubakar Kulima jami'in tsaro ne daga cikin jami'an hadin guiwa na CJTF. Ya ce maharan sun dinga harbe-harbe kuma sun yi awon gaba da dabbobi a kauyen, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Kotu ta tsinke aure bayan miji ya yi yunkurin amfani da mata wurin tsafi
"Al'amarin kullum yana zama abun tsoro kuma idan har za su iya zuwa kauyen Moromti, toh tabbas Bulumkutu bata tsira ba. Mun kaiwa hukuma rahoto," Kulima yace.
Wani mazaunin kauyen Moromti, Mustapha Umaru, ya tabbatar da cewa mazauna kauyen sun bar gidajensu domin neman mafaka.
"Mun ji harbin bindiga kuma mazauna kauyen sun zo Moromti inda suka kwana. An kwashe musu akuyoyi, kaji da raguna.
"Sun kara da kwashe sabbin kaya daga kauyen. Sun tafi da kekuna tare da kwashe kayan abinci," Mustapha yace.
Wata majiya daga 'yan sanda wacce ta bukaci a sakaya sunanta ta tabbatar da aukuwar lamarin.
KU KARANTA: Bidiyon 'yar majalisa matar aure ɗare-ɗare a cinyar dan majalisa ya janyo cece-kuce
A wani labari na daban, rundunar sojin sama ta Operation Lafiya Dole ta yi wa 'yan ta'addan Boko Haram mummunar barna a dajin Sambisa da ke jihar Borno.
Ta ragargaza maboyar wasu manyan shugabannin 'yan ta'addan da ke Alagarno wanda aka gano shugabannin ne kadai ke zama a wurin.
Wurin na boye a kasan bishiyoyi kuma yana da nisan kilomita 2.3 arewa maso gabas daga KAFA, inda 'yan ta'addan ke amfani da shi wurin shirya makircinsu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng