Ragakafin korona: Buhari ya ce ayi wa manyan mawaka, Limamai da fastoci allurar kai tsaye ta akwatin talbijin kowa ya gani

Ragakafin korona: Buhari ya ce ayi wa manyan mawaka, Limamai da fastoci allurar kai tsaye ta akwatin talbijin kowa ya gani

- Za a nuno wasu jerin manyan yan Najeriya kai tsaye a akwatin talbijin yayinda suke karbar allurar rigakafin korona

- Shugaba Buhari ya yarda ayi wa manyan yan Najeriya da dama a bangaren addini, wasanni da nishadantarwa allurar kowa ya gani

- Gwamna Fayemi na Ekiti ya ce an yi hakan ne domin karfafa wa jama’a gwiwar karbar rigakafin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana so Limamai, manyan fastoci, manyan mawaka da yan wasanni a kasar su karbi allurar rigakafin korona kai tsaye a akwatin talbijin.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar Shugaban kasa bayan ganawa da shugabannin Najeriya a ranar Juma’a, 8 ga watan Janairu a Abuja.

A cewar wani rahoto daga jaridar Daily Sun, Gwamna Fayemi ya ce shugaba Buhari na so kwamitin fadar shugaban kasa kan korona ya kara manyan yan Najeriya cikin jerin wadanda za su karbi rigakafin kai tsaye a akwatin talbijin.

Ragakafin korona: Buhari ya ce ayi wa manyan mawaka, Limamai da fastoci allurar kai tsaye ta akwatin talbijin kowa ya gani
Ragakafin korona: Buhari ya ce ayi wa manyan mawaka, Limamai da fastoci allurar kai tsaye ta akwatin talbijin kowa ya gani Hoto: @kfayemi
Asali: Twitter

A cewar shugaba Buhari, hakan zai karfafa gwiwar jama’a wajen sanin cewa rigakafin bai da illa.

KU KARANTA KUMA: Rashida Mai Sa’a tayi zazzafan raddi ga yan matan Kannywood kan zuwa yawon bude ido a Dubai

Fayemi ya ce:

“Shugaban kasa ya yarda da ni cewa zai sanar da kwamitin PTF fa’idar amfani da sauran masu fada aji, imma manyan Limamai, fastoci, manyan mawaka da yan wasan kwallon kafa.

“Saboda ganin irin wadannan mutane suna karbar rigakafin zai sa ya kara karbuwa a garuruwanmu."

Gwamnan na kudu maso yamma ya kuma jinjinawa fadar Shugaban kasa da PTF kan jagoranci nagari da kuma karbar rigakafi kai tsaye a talbijin.

KU KARANTA KUMA: Rarara ya gwangwaje jaruman Kannywood da kyautar sabbin motocin alfarma

A gefe guda, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kara tsawon wa'adin kwamitin yaki da annobar korona

A cewar jagora a kwamitin, Dakta Sani Ali, shugaba Buhari ya bayar da umarnin a samar da alluran rigakafin korona.

Dakta Sani ya kara da cewa Buhari ya bayar da umarnin cewa a yi wa 'yan Nigeria allurar rigakafin kyauta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel