NDLEA ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara da za a dauka aiki

NDLEA ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara da za a dauka aiki

- Hukumar NDLEA ta fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasara da za a dauka aiki

- NDLEA ta ce su duba shafinta na yanar gizo domin ganin bayanin abubuwan da ake bukata daga gare su

- Za a fara tantance wadanda suka yi nasarar daga ranar 10 zuwa 23 ga watan Janairun 2021 a Jihar Plateau

Hukumar Hana Fataucin Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta fitar da jerin sunayen wadanda suka yi nasara cikin masu neman shiga aiki a hukumar.

Mai magana da yawun rundunar, DCN Jonah Achema ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma'a a Abuja, News Wire ta ruwaito.

NDLEA ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara da za a dauka aiki
NDLEA ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara da za a dauka aiki. Hoto: @NewsWireNGR
Asali: Twitter

Ya ce wadanda suka nemi shiga aikin su ziyarci shafin yanar gizo ta hukumar a www.ndlea.gov.org domin ganin jerin sunayen wadanda suka yi nasara, ya kara da cewa an kuma aike musu sakon tes de imel.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Sanata Adebayo Salami rasuwa

Ya kara da cewa masu neman shiga aikin sun neme matsayi daban daban.

"Ana umurtar wadanda suka yi nasara, su kimanin 5000, su zo Makarantar Bada Horaswa na hukumar ta Citadel Counter-Narcotics Nigeria, (CCNN), Katton-Rikkos, Jos, Jihar Plateau domin tantancewa da bada takardunsu daga ranar 10 ga watan Janairun 2021 zuwa 23 misalin karfe 9 na safe a kullum.

"An raba masu zuwa tantancewar gida hudu saboda kiyayye dokokin dakile yaduwar korona.

"An sanar da tsarin yadda aka raba su. Ana sa ran su iso kwana guda kafin ranar tantance su," in ji Mr Achema.

KU KARANTA: NIN: Ma'aikatan NIMC sun fara yajin aiki saboda fargabar korona

Ana umurtar wadanda suka yi nasara su taho da takardar tabbatar da lafiyarsu da suka karbu daga asibitin gwamnati da sauran takardun karatu.

Har way yau, sanarwar ta ce wadanda suka yi nasarar su zo da fom din garanto, takardun karatu, haihuwa da ta karamar hukuma tare da fotokopi.

Ana kuma sa ran su taho da gajerun wanduna, riga shirt, takalmin canvas da safa in ji kakakin hukumar.

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164