PTF: Buhari ya umarci a yi wa 'yan Nigeria rigakafin korona kyauta
- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kara tsawon wa'adin kwamitin yaki da annobar korona
- A cewar jagora a kwamitin, Dakta Sani Ali, shugaba Buhari ya bayar da umarnin a samar da alluran rigakafin korona
- Dakta Sani ya kara da cewa Buhari ya bayar da umarnin cewa a yi wa 'yan Nigeria allurar rigakafin kyauta
A ranar Laraba ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kara tsawon wa'adin aikin kwamitin yaki da cutar korona (PTF) da ya kafa tun farkon barkewar annobar.
Dakta Sani Ali, jagoran kwamitin PTF, ya ce 'yan Nigeria za su sha allurar rigakafin cutar korona kyauta da zarar gwamnati ta karbi alluran a watan Janairu.
Yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels ranar Laraba, Dakta Aliyu, ya ce shugaba Buhari ne ya umarci a yi hakan yayin ganawarsu, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
Ya ce gwamnati ta yi shiri mai kyau da tsare-tsare masu karfi domin tabbatar da cewa an wayar da kan 'yan kasa sun rungumi rigakafin da zuciya daya.
KARANTA: Fadar shugaban kasa: Ana shiryawa Buhari wata makarkashiya mai kama da juyin mulki
"Shugaban kasa ya umarci kwamitinmu ya cigaba da aikinsa har zuwa farkon sabuwar shekara.
"Kazalika, ya umarcemu mu tabbatar an samar da rigakafin annobar a Nigeria kuma za'a yi wa kaso 20 cikin 100 na 'yan Nigeria kyauta, ba tare da sun biya ko sisi ba," a cewarsa.
KARANTA: Kage da kazafi: IGP Adamu ya shigar da karar dan takarar shugaban kasa a 2019
Dakta Aliyu ya bayyana cewa PTF zai hada kai da ma'aikatar ilimi da hukumomin da suka dace domin wayar da kan jama'a a kan allura rigakafin annobar korona.
Shafin Legit.ng ya samo muku wasu ingantattun bayanai da ya kamata kowanne ɗan Najeriya ya sani dangane da wannan magani na rigakafin korona, kamar yadda muka wallafa a baya.
A ƙarshe, an samar da ingantaccen maganin riga-kafin cutar COVID-19 a ƙasar Amurka, Burtaniya da wasu manyan ƙasashe da ke faɗin duniya.
Alamu sun tabbatar da samun sauki daga wannan magani duk da cewa cutar na sake dawowa a karo na biyu. Sai dai duk da haka, riga-kafin na iya kare mutum daga sake kamuwa da cutar duk da akwai alamun tambayoyi kan hakan
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng