Wani dan shekara 83 zai yi wuff da yarinya mai shekaru 16

Wani dan shekara 83 zai yi wuff da yarinya mai shekaru 16

- Wani dattijo mai shekaru 83, Alhaji Yushu'u Suleiman zai angwance da yarinya mai shekaru 16, Amina Mohammed

- Kamar yadda katin daurin auren ya nuna, za a daura auren ne a yau Asabar 9 ga watan Janairu

- Wata Hajiya Kande daga karamar hukumar Wushihi na Jihar Niger ne ta dauki nauyin yin katin gayyatar

Wani kafar watsa labarai na yanar gizo a Jihar Niger ya wallafa wannan hoton gayyatar daurin aure wani mutum dan shekaru 83 mai suna Alhaji Yushu'a Suleiman da wata yarinya, Amina Mohammed da aka ce shekarunta 16.

A takardan gayyatar, an shirya daurin auren ne a ranar Asabar 9 ga watan Janairun 2021, amma, ba a bayyana Jihar da za a daura auren ba.

Wani dan shekaru 83 zai yi wuff da yarinya mai shekaru 16
Wani dan shekaru 83 zai yi wuff da yarinya mai shekaru 16. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Sanata Adebayo Salami rasuwa

Wata Hajiya Kande daga karamar hukumar Wushishi na Jihar Niger ne ta dauki nauyin yin katin gayyatar daurin auren.

Kamar yadda ya ke a hoton, dattijon na sanye da fararen kaya da rawani da tabarau yayin da ita kuma yarinya tana sanye da atampa.

KU KARANTA: Hanan Buhari tare da mijinta Turad sun tafi Dubai don bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Bidiyo da Hotuna)

Babu lambar wayar wasu daga cikin masu dawainiyar daurin auren kamar yadda aka saba saka wa a katin wasu gayyatan sai dai lambar wadanda suka buga katin shima bai fito da kyau ba saboda yanayin daukan hoton.

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164