Elon Musk ya zama mutumin da ya fi kowa arziki a duniya

Elon Musk ya zama mutumin da ya fi kowa arziki a duniya

- Elon Musk, daya daga cikin wanda suka kafa kamfanin Tesla ya sha gaban Jeff Bezos ya zama mutumin da ya fi kowa arziki a duniya

- Elon Musk ya bawa shugaban Amazon, Jeff Bezos ratar Dala biliyan 1.5 (N571,800,000,000) sakamakon habbakar da hannun jarin kamfaninsa ta yi da 4.8%

- Kafin samun wannan karin arzikin, Musk ya samu alheri sosai a shekarar 2020 saboda habbakar da hannun jarin Tesla ta samu a kasuwar duniya

Bayan watanni masu yawa, Elon Musk na kamfanin Tesla ya zama mutumin da ya fi kowa arziki a duniya ya sha gaban Jeff Bezos mai kamfanin Amazon.

Ya samu wannan nasarar ne saboda habbakar da hannun jarin kamfanin Tesla Inc ta yi a ranar Alhamis 7 ga watan Janairu, wadda hakan ya saka Elon cikin mutane 500 da suka fi arziki a duniya kamar yadda Bloomberg ta ruwaito.

Elon Musk ya zama mutumin da ya fi kowa arziki a duniya
Elon Musk ya zama mutumin da ya fi kowa arziki a duniya
Asali: Getty Images

A karfe 10:15 na safiyar yau, Musk ya mallaki Dalla biliyan 188.5 (N71,856,200,000,000.02) sakamakon ribar da ya samu na Dalla biliyan 1.5 (N571,800,000,000) fiye da shugaban na Amazon.

DUBA WANNAN: 'Yan majalisar Ghana sun bawa hammata iska kan batun rinjaye (Bidiyo)

An ruwaito cewar a farashin hannun jarin kamfanin Tesla ya karu da 4.9% a ranar Laraba, 6 ga watan Janairu inda ya bawa Musk ikon shan gaban Bezos da Dalla biliyan 3 (N1,143,600,000).

Tun watan Oktoban shekarar 2017, Jeff Bezos ne ke rike da kambun mutumin da ya fi kowa arziki a duniya. Sabon mai kudin na duniya Musk, kuma yana da hannun jari a kamfanin Space X.

KU KARANTA: Daga Mali da Sudan ake ɗako hayar yan bindigan da ke adabar arewa, Gwamna Sani-Bello

Muhimmin abinda ya taimakawa Musk samun ikon shan gaban Bezos shine irin ribar da ya samu a shekarar 2020 sakamakon habbakar da hannun jarin Tesla ta yi da 743%.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164