NIN: Ma'aikatan NIMC sun fara yajin aiki saboda fargabar korona
- Ma'aikatan hukumar NIMC sun tsunduma yajin aiki bisa tsoron kamuwa da COVID-19 da kuma rashin biyan su hakkokin su
- Yajin aikin na zuwa daidai lokacin da wa'adin datse layukan da ba a hada rijistar da lambar dan kasa ba ya kusa cika
- Sun ce har yanzu ba a dauki wani mataki kan ma'aikatan su da suka kamu da coronavirus ba saboda haka baza su iya ci gaba da daukar hadari ba
Dubban mutane aka bari na shan sanyi a wajen ofisoshin hukumar katin dan kasa bayan ma'aikatan hukumar sun tsunduma yajin aiki, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sanarwar yajin aikin na dauke da sa hannun shugaban manyan ma'aikatan gwamnati, reshen hukumar NIMC, Lucky Michael, da sakataren ta, Odia Victor.
DUBA WANNAN: 'Yan majalisar Ghana sun bawa hammata iska kan batun rinjaye (Bidiyo)
Wani bangaren sanarwar ya ce, "biyo bayan tattaunawa da wannan kungiya ta gudanar ranar 6 ga Janairu, 2021, shugabannin reshen kungiya na umartar duk mambobinta daga mataki na 12 zuwa kasa a manyan ofisoshi da kuma ofisoshin jiha da su fita aiki a gobe 7 ga Janairun 2021 amma kada su yi aiki.
"Duk mambobin ofisoshin kananan hukumomi su kauracewa wuraren aikin su kuma akwai kwamitin sa ido da zai dinga zagaye don tabbatar da cika umarnin."
Hukumar sadarwar ta kasa ce dai ta umarci kamfanonin sadarwa da su datse duk wani layi da bai hada rijistar layin sa da lambar dan kasa ba kafin karshen Janairu.
KU KARANTA: Zaben kananan hukumomi: 'Yan takara 6 sun fadi gwajin miyagun kwayoyi a Kano
Yanzu haka dai, fiye da mutane miliyan 100 ba su kai ga cika umarnin ba, lamarin da ya haddasa cinkoso a ofisoshin hukumar NIMC tare da sabawa ka'idojin COVID-19.
Acewar wata sanarwa da aka fitar a ƙarshen taron ACCSN, reshen NIMC, yajin aikin ya zama dole sakamakon haɗarin kamuwa da cutar COVID-19 da ma'aikatan hukumar NIMC ke fama da shi.
Sannan an gaza basu kayan kariya,ga rashin ƙarin matsayi da kuma ƙarancin kuɗaɗe.
Sun kuma nemi da ake biyansu kuɗaɗen ƙarin lokacin aiki,sannan a basu isassun kayayyakin aiki da zasu yi aiki da su.
Gamayyar ma'aikatan, "Ma'aikatan mu sun kamu da COVID-19 kuma har yanzu ba'a ɗauki wani mataki don daƙile yaɗuwar cutar."
"Taron ya nuna lafiyar ma'aikata ita ce gaba da komai.
Baya ga haka a gaggauta yiwa ofisoshin feshin magani cikin hanzari."
"Gamayyar ma'aikatan sun yarda akan gwamnati ta gyara tsarin biyan albashin ma'aikatan NIMC wanda mataimakin shugaban ƙasa ya kawo tsarin gyara albashin su a kasafin 2021 wanda zai fara daga watan Junairun 2021.
"Hakazalika،a duba ɗungushe da munamunar ƙarin girma da aka yiwa ma'aikatan tsakanin shekarar 2017 zuwa 2020,sannan ayi gyara dai-dai da tsarin da kundin dokar ma'aikatan gwamnati."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng