Daga Mali da Sudan ake ɗako hayar yan bindigan da ke adabar arewa, Gwamna Sani-Bello

Daga Mali da Sudan ake ɗako hayar yan bindigan da ke adabar arewa, Gwamna Sani-Bello

- Abubakar Sani Bello, gwamnan Jihar Niger ya ce akwai yan bindiga da aka dako daga kasashen Mali da Sudan suna barna a arewacin Najeriya

- Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a gidan gwamnati

- Gwamna Sani Bello ya ce ya tafi fadar shugaban kasar ne domin neman taimakon gwamnatin tarayyar wurin yaki da yan bindigan

Gwamnan Jihar Niger Abubakar Sani-Bello, a ranar Laraba, ya ce 'yan bindiga daga kasashen Mali da Sudan suna kai hare-hare a wasu yankunan Arewa, The Nation ta ruwaito.

A cewarsa, yan bindigan sun shigo kasar ne a kan babura kuma a dandalin sada zumunta ake nemansu - musamman Facebook.

Daga Mali da Sudan ake ɗako hayar yan bindigan da ke adabar arewa, Gwamna Sani-Bello
Daga Mali da Sudan ake ɗako hayar yan bindigan da ke adabar arewa, Gwamna Sani-Bello. Hoto: @TheNationNews
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan majalisar Ghana sun bawa hammata iska kan batun rinjaye (Bidiyo)

Gwamnan na Jihar Niger, wadda ya bayyana hakan a ranar Laraba, ya ce ya mika batun da wasu kallubalen tsaro da jiharsa ke fuskanta ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya yi magana da manema labarai a gidan gwamnati bayan ganawarsa da shugaban kasa.

Niger na daya daga cikin jihohin Arewa da ke fama da kallubalen 'yan bindiga.

Sani-Bello ya kara da cewa wasu yan bindiga daga jihohin Zamfara da Kaduna suna kai hare-hare jiharsa.

KU DUBA: Amsar Rahama Sadau game da batun dena fim bayan aure

Ya kara cewa, baya ga matsalar yan bindiga da wasu laifuka, batun rashin abinci, kona daji da kashe dabobi na cikin abubuwan da ke addabar jihar.

Gwamnan ya yi bayanin cewa ya ziyarci Shugaba Buhari ne domin neman tallafin gwamnatin tarayya kan batun yan bindiga da gyaran tituna da suka lalace a jiharsa.

Wani sashi cikin jawabin gwamnan "Matsalar babba ne. Neja na da girman kilomita 73,000. Girman Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas kenan (Idan an gwamutsa su). Da farko, muna da karancin jami'an tsaro kuma ina ganin ya kamata mu kara adadinsu da za su yi aiki a dukkan sassan jihar.

"Muna samun yan bindiga suna shigowa daga jihohin da ke makwataka da mu musamman Zamfara da Kaduna. Yana da wahala a tsare dazukan don motoccin mu ba zasu iya shiga dajin ba, don haka muna taimakon gwamnatin tarayya musamman sojojin sama. Sojojin saman na bada taimako sosai kuma suna samun nasarori."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel