'Yan bindiga sun kashe mutane 4 a kauyen Kaduna
- Yan bindiga sun kashe mutane 4 tare da yin garkuwa da mata a kauyen Katarma a Jihar Kaduna
- Kwamishinan tsaro, Aruwan ya ce an ceto gaba daya matan da aka yi garkuwa da su
- Akwai jami'an sintiri daga cikin mutanen da yan bindigar suka kashe
'Yan bindiga sun kai hari ranar Laraba kauyen Katarma a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna, tare da kashe mutum hudu ciki harda jami'an sintiri kafin su yi garkuwa da wasu mata a yankin, Daily Trust ta ruwaito.
A rahoton jami'an tsaro, jami'an sintiri ne suka fara tunkarar yan bindigar kafin daga bisani jami'an tsaro su shiga kauyen.
Mutane hudun da lamarin ya shafa sune Bulus Barde, Hassan Zarmai, Lawal Pada da kuma Kefas Auta wanda aka kashe a musayar wuta.
Sauran mutum uku, Amos Doma, Zamba Ali da Bomboi Busa sun samu raunika a musayar wutar.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa, ya ce an ceto gaba daya matan da aka sace.
A cewar sa, da ake mayar da martanin harin, an tura rundunar sojojin sama kauyen Katarma da Kusasu da ke jihar Niger.
Su kuma sojojin kasa suka ci gaba da bibiyar su yayinda sojojin sama suka kashe yan bindiga da dama.
Aruwan ya ce an hangi yan bindiga a Katarma, wanda suka tara garken shanu suna kokarin guduwa akan babura.
"Jami'an sojin sama sun kashe su ta jirgi"
A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.
Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.
A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng