Ana binmu ana kashewa, amma an ki yin komai, don haka mu ka bar Jihar Ebonyi
- Wani Makiyayi ya ce addabar da ake yi masu ta sa su ka bar Jihar Ebonyi
- ‘Yan Sanda su na cewa Fulani sun bar Ebonyi ne don ganin damarsu kawai
- Wannan Makiyayi ya ce tsabar matsin lambar da ake yi masu ce ta kora su
Wasu gungun makiyaya Fulani da ke kiwo a Ebonyi, sun yi hira da ‘yan jarida, suka bayyana ainihin dalilan da su ka sa su ke barin jihar Kudun.
Wadannan makiyaya sun shaidawa BBC Hausa cewa ana gallaza masu, har abin ya kai ga kashe masu mutane, don haka suka zabi su bar jihar Ebonyi.
Premium Times ta ce wadannan Fulani sun fadawa BBC Hausa cewa an ki daukar matakin kirki duk da an sanar da hukuma halin da su ke ciki a jihar.
Makiyayan sun bayyana cewa a shekarar 2020, an hallaka makiyaya Fulani akalla 21, sannan an kona gidajensu kurmus, ba tare da sun yi wani abu ba.
KU KARANTA: Kaduna: An sace matan aure da wasu mutane a Giwa
A cewar makiyayan, gwamnati da jami’an tsaro ba su ga damar hukunta masu laifin nan ba.
Wani makiyayi ya fadawa BBC: “Ba a dade ba, suka dawo suka kashe mana shanu biyu. Bayan nan ana yi mana barazanar cewa za a kona gidajenmu.”
Wannan dattijo ya ce an kai wa wasu ‘yanuwansu a wani yankin jihar Ebonyi mummunan hari.
“A dalilin haka muna zaman dar-dar. Duk lokacin da muka fita, iyalanmu suna tsoron a kawo masu hari, wannan ya sa muke kaura.” Inji wannan mutumi.
KU KARANTA: Makiyaya sun mutu a harin da aka kai a rugar Fulani a Ebonyi
Da aka tambaye shi game da zargin yin ta’adi, dattijon ya musanya wannan, sannan ya karyata ikirarin hukuma na cewa ganin damarsu ta sa su ka tashi.
A makon nan kun ji cewa kungiyar gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya ta zargi masu siyasa ido-rufe da hada kai da 'yan bindiga don kawo hargitsi.
Channels ta rahoto shugaban kungiyar kuma gwamnan Ebonyi, Dave Umahi ya na wannan bayani.
Dave Umahi ya ce wadannan 'yan siyasa su na neman cinma mugun nufinsu ko ta wani hali, sannan ya ce babu yunkurin fatattakar Fulani daga Ebonyi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng