Kasafin kudin 2021: N2.42bn na tafiye-tafiye, N135m na lemuka aka warewa fadar Buhari

Kasafin kudin 2021: N2.42bn na tafiye-tafiye, N135m na lemuka aka warewa fadar Buhari

- Ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kashe N2.42bn a kan tafiye-tafiye a 2021

- Hakazalika, ofishin zai kashe naira miliyan 135.6 a kan lemuka duk a shekarar 2021

- An warewa ofishin shugaban Buhari N3.82bn na manyan ayyuka sai N2.76bn na ayyukan yau da kullum

Ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kashe naira biliyan 2.42 a kan tafiye-tafiye na cikin gida da kasashen ketare a 2021 yayin da fadar shugaban kasa za ta kashe N135.6 miliyan a kan lemuka kamar yadda jaridar The Cable ta gani a kasafin kudi.

A ranar 31 ga watan Disamban 2020 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan kasafin kudin kasar nan na 2021.

A kasafin kudin, jimillar kudin da aka warewa ofishin shugaban kasan na manyan ayyuka shine N3.82bn sai N2.76bn na ayyukan yau da kullum.

KU KARANTA: Farashin hatsi: Bude iyakokin tudun kasar nan ya ragargaza farashin kayan abinci

Kasafin kudin 2021: N2.24bn na tafiye-tafiye, N135m na nishadi aka ware wa Buhari
Kasafin kudin 2021: N2.24bn na tafiye-tafiye, N135m na nishadi aka ware wa Buhari. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Sauran abubuwan da aka hango a kasafin kudin na 2021 shine kayan abinci da sauran kayan girki na ofishin shugaban kasan zai kwashe N98.3 miliyan, alawus na zama zai lashe N164.17 miliyan yayin da N41.21 miliyan za ta tafi wurin talla da hulda da jama'a.

A ofishin mataimakin shugaban kasa, za a kashe N801.03 miliyan na tafiye-tafiyen cikin gida da kasashen ketare, lemuka da abinci za su lashe N18.26 miliyan, alawus na zama zai kwashi N20.26 miliyan.

An ware N50.88 miliyan domin samar da kayan abinci da na hadinsu sai kayayyakin walwala za su kwashe N23 miliyan.

Ofishin zai kashe N111.7 miliyan na siyan na'urori masu kwakwalwa a wannan shekarar.

KU KARANTA: Ganduje zai koma biyan N18,000 karancin albashi, ya bayyana dalilinsa

A wani labari na daban, hukumar Hisbah ta jihar Kano ta damke wasu matasa a kan zarginsu da take da hannu cikin al'amuran rashin da'a a birnin Kano, Premium Times ta wallafa.

Kakakin hukumar Hisbah na jihar Kano, Lawal Ibrahim, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba a Kano ya ce an kama su ne sakamakon wani samame da aka kai.

Kamar yadda yace, an kama wadanda ake zargin a daren Talata a lamido Crescent da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano a kan siyar da miyagun kwayoyi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng