Farashin hatsi: Bude iyakokin tudun kasar nan ya ragargaza farashin kayan abinci

Farashin hatsi: Bude iyakokin tudun kasar nan ya ragargaza farashin kayan abinci

- Bude iyakoki 4 na kasar nan da gwamnatin tarayya tayi ya taka rawar gani wurin ragargaza farashin kayan masarufi

- 'Yan kasuwan da ke siyan kayan masarufi su adana da zummar kayan sai sun yi tsada su fitar, yanzu sun dena

- Suna tsoron siya bayan nan gwamnatin tarayya ta dage dokar hana shigo da shinkafa tare da sauran kayan abinci

Bude iyakokin tudun kasar nan hudu da gwamnatin tarayya tayi a makon da ya gabata ya taka rawar gani wurin ragargaza farashin hatsi da sauran kayan abinci.

Hakazalika hakan ya dakatar da al'amura masu tarin yawa a kasuwanni jihar Katsina, Katsina Post ta wallafa.

Kafin sanar da bude iyakokin tudun, 'yan kasuwar hatsi da wasu 'yan kasuwa suna boyewa da sunan wakilan kamfanoni inda suke siyan kayan gona da yawa kuma suke boyewa domin samun riba a nan gaba.

KU KARANTA: BUK ta soke zangon karatu na 2019/2020, ta sanar da ranar komawar dalibai

Farashin hatsi: Bude iyakokin tudun kasar nan ya ragargaza farashin kayan abinci
Farashin hatsi: Bude iyakokin tudun kasar nan ya ragargaza farashin kayan abinci. Hoto daga Katsinapost.com.ng
Asali: UGC

Kamar yadda diloli suka sanar, duk da hana shigo da shinkafa tare da kayan abinci. A halin yanzu 'yan kasuwan suna tsoron siyan kayan su ajiye gudun kada gwamnati ta sauya ra'ayinta tare da dage hukuncinta nan gaba.

Hakazalika, Mallam Muhammadu Tarzana wanda ya kasance babban mai siyar da hatsi a kasuwar Bakori, ya ce wannan sanarwar bude iyakokin tudun sun matukar taka rawar gani wurin ragargaza farashin kayan abinci.

"A shekarar da ta gabata, buhun masara ana siyar da shi a N8,000 zuwa N9,500, dawa ana siyar da ita a N14,000 zuwa N13,000.

"Sanarwan bude iyakokin kasar nan ya ragargaza farashin shinkafa mai bawo zuwa N14,000 ko N12,000 buhu daya, dawa N14,500 zuwa N13,000 sai kuma masara daga N15,500 zuwa N14,000"

Tarzana ya kara da cewa da yawa daga cikin 'yan kasuwan sun daina siyan kayan masarufin da yawa bayan sanarwar saboda suna tsammanin gwamnatin tarayyar ta daga kafa a kan hana shigo da kayan abinci.

KU KARANTA: Kyakyawar budurwa lauya ta ce ta gaji da zama babu miji, tana bukatar wanda za su ci dukiyarta tare (Hotuna)

A wani labari na daban, Sanata Ibrahim Shekarau da Sanata Rabiu Musa Kwankwasoo, dukkansu tsofaffin gwamnonin jihar Kano sun kasance tsoffin makiya a siyasance wadanda basu iya zama a inuwa daya ballantana a siyasa.

Shekarau ya kayar da Kwankwaso a 2003 a lokacin da Kwankwaso yake neman zarcewa. Kwankwaso ya yi nasarar a 2011 inda ya kayar da Salihu Sagir Takai a zaben gwamnoni.

Kwankwaso ya sake nasara bayan Ganduje dan takararsa ya maka Takai dan takarar Shekarau da kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: