Hukumar Hisbah ta cafke matasa 53 a kan laifin aikata al'amuran rashin da'a

Hukumar Hisbah ta cafke matasa 53 a kan laifin aikata al'amuran rashin da'a

- Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta kama wasu matasa 53 a tsakar birnin Kano

- Kakakin hukumar, Lawal Ibrahim, ya tabbatar da kama su a ranar Talata da dare

- Ya ce an kama su da laifiin ta'ammali tare da siyar da miyagun kwayoyi a jihar

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta damke wasu matasa a kan zarginsu da take da hannu cikin al'amuran rashin da'a a birnin Kano, Premium Times ta wallafa.

Kakakin hukumar Hisbah na jihar Kano, Lawal Ibrahim, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba a Kano ya ce an kama su ne sakamakon wani samame da aka kai.

Kamar yadda yace, an kama wadanda ake zargin a daren Talata a lamido Crescent da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano a kan siyar da miyagun kwayoyi.

KU KARANTA: In har liyafar badala ta sa aka rushe otal, gidan dan El-Rufai ya dace a fara rushewa, Reno Omokri

Hukumar Hisbah ta cafke matasa 53 a kan laifin aikata al'amuran rashin da'a
Hukumar Hisbah ta cafke matasa 53 a kan laifin aikata al'amuran rashin da'a. Hoto daga @Premiumtimes
Source: Twitter

"Wadanda ake zargin sun hada da maza 27 tare da mata 26 dukkansu masu shekaru tsakanin 17 zuwa 19.

"Jami'anmu sun fita wurin karfe 10 na dare kuma sun cafko mutane 53 da ake zargi," yace.

Ibrahim wanda yace an tantance dukkan wadanda ake zargin, ya ce, "mun gano cewa dukkansu wannan ne karonsu na farko da suka aikata laifin. An yi musu nasiha tare da mika su hannun iyayensu."

Ya ce kwamandan Hisbah, Harun Ibn-Sina, ya ja kunnen matasan jihar da su gujewa aikata miyagun ayyuka kuma su zama 'yan kasa nagari.

KU KARANTA: Bidiyon Kakan da ya kai jikonkinsa gwajin DNA, ya gano ba shi ya haifa mahaifinsu ba

A wani labari na daban, Annobar korona ta yi mummunar illa ga tattalin arzikin jihohi da dama na Najeriya ballantana jihar Kano.

Hakan yasa gwamnatin jihar Kano ta sanar da komawa biyan ma'aikatanta karancin albashin N18,000 a maimakon N30,000 da ta fara bayan boren da kungiyar kwadago tayi, The Cable ta ruwaito.

A yayin tabbatar da wannan cigaban, mai magana da yawun Gwamna Umaru Ganduje, Salihu Tanko-Yakasai, ya ce halin da kasar nan ta shiga sakamakon annobar korona ce ta saka hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel