Ganduje zai koma biyan N18,000 karancin albashi, ya bayyana dalilinsa

Ganduje zai koma biyan N18,000 karancin albashi, ya bayyana dalilinsa

- Gwamnatin jihar Kano ta sanar da daina biyan ma'aikatanta karancin albashin N30,000

- Jihar ta gaggauta komawa biyan karancin albashin zuwa N18,000 a ranar 6 ga watan Janairu

- Gwamnatin ta bayyana cewa hakan ya biyo bayan karayar tattalin arzikin da aka shiga saboda Covid-19

Annobar korona ta yi mummunar illa ga tattalin arzikin jihohi da dama na Najeriya ballantana jihar Kano.

Hakan yasa gwamnatin jihar Kano ta sanar da komawa biyan ma'aikatanta karancin albashin N18,000 a maimakon N30,000 da ta fara bayan boren da kungiyar kwadago tayi, The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA: Bidiyon Kakan da ya kai jikonkinsa gwajin DNA, ya gano ba shi ya haifa mahaifinsu ba

Ganduje zai koma biyan N18,000 karancin albashi, ya bayyana dalilinsa
Ganduje zai koma biyan N18,000 karancin albashi, ya bayyana dalilinsa. Hoto daga @Dawisu
Asali: UGC

A yayin tabbatar da wannan cigaban, mai magana da yawun Gwamna Umaru Ganduje, Salihu Tanko-Yakasai, ya ce halin da kasar nan ta shiga sakamakon annobar korona ce ta saka hakan.

Ya ce: "Gwamnatin jihar ta koma biyan tsohon karancin albashi saboda halin da ta shiga. Abinda muke samu a matsayin gwamnati yanzu ya ragu kuma ba za mu iya cigaba da biyan N30,000 ba a matsayin karancin albashin."

Amma kuma, ma'aikatan gwamnatin da ke jihar sun jajanta yadda gwamnatin jihar bata bada wata sanarwa ba kafin ta fara zabtare musu albashi.

KU KARANTA: Kabilar Yarabawa: Camfi da al'adu 9 da baka taba jin labarinsu ba

A wani labari na daban, 'yan bindiga masu tarin yawa sun cimma ajalinsu sakamakon samamen tudu da na jiragen yaki da soji suka kai musu a Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun a jihar Kaduna, Vanguard ta wallafa.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar ya ce dakarun sun tabbatar da samamen da suka kai a ranar Litinin a Albasu, Rahama, Sabon Birni, Rikau, Fadama kanauta, Galadimawa, Kaya, Kidandan, Yadi, Dogon Dawa, Ngede Allah, Damari, Saulawa, Takama, Kuduru, Ungwan Yakoda babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari.

"An ga 'yan bindiga a Yadi kuma an ragargaji yankin ta sama sannan an kashesu da yawansu," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel