Dan yawon bude ido ya sullube zuwa cikin makeken rami mai zurfin kafa 350 yayin daukan hoto
- Wani magidanci dan yawon bude ido ya sulluba zuwa cikin wakeken rami mai zurfin kafa 350 yayin da ya ke daukar hoto
- Rahotanni sun bayyana cewa mutumin mai suna Roy George Tinashe Dikinyay ya ziyarci tsaunin Victoria Falls tare da iyalinsa
- Jami'an ceto sun sha wahala kafin gano sassan jikin Roy sakamakon tarwatsewar da gangar jikinsa ta yi bayan fadawarsa
Wani mai yawon buɗe ido a kasar Zimbabwe, Roy George Tinashe Dikinyay, ya faɗo daga saman tsauni jim kaɗan bayan ya turo hoton sa a saman tsaunin mai nisan kafa 350 zuwa kasa.
A cewar rahotan jaridar The Nation, mutumin ya na tsaye ne a gefen tsaunin Victoria Falls daidai lokacin da ya juya ga iyalansa don sake ɗaukar hotuna na yadda ruwa ke kwaranyowa.
A wani hoto na biyu da ya ɗauka, ya nuna mutumin na sanye da takalmi sandal a gaɓar tsaunin inda ya ke ɗauke da wasu abubuwa a hannunsa.
Hukumomin masu kula da wuraren yawon buɗe ido da masu ceto da bayar da agajin gaggawa sun ce an samu sassan jikin mutumin tsakanin wasu duwatsu da ke da nisan kafa 350 daga inda ya faɗo.
KARANTA: Da gyara a jawabinka na sabuwar shekara; Dattijan arewa sun aika sako ga Buhari
"Wasu sassan jikin nasa sun makale a duwatsu" in ji mai magana da yawun hukumar.
KARANTA: Ina kisa ne domin kawai na samu kudin shan giya da shagwaba budurwata - Matashi Tajudeen
Ya cigaba da cewa, "Yanzu haka muna kan tuntubar kwararrun jami'an tsaro don ciro sauran sassan jikin nasa"
Hukumomin suna son yin amfani da jirgi mai saukar ungulu na sojin kasar don gano sauran sassan jikin mutumin.
A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, alamu na nuna cewa da yawa daga cikin ɗaliban jami'ar BUK ba za su koma karatu a ranar 18 ga Janairu ba kamar yadda hukumar gudanarwar jami'ar ta sanar.
Kwana ɗaya da sanarwar janye yafin aiki na tsawon wata tara da ƙungiyar malaman jami'o'in ƙasar nan ta yi, da yawan ɗaliban jami'o'i sun nuna rashin shirinsu na komawa makarantar a lokacin da aka sanar.
Wasu daliban Jami'ar da aka tattauna da su sun bayyana cewa da sauran rina a kaba, su ma basu shirya komawa makaranta ba.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng