Da gyara a jawabinka na sabuwar shekara; Dattijan arewa sun aika sako ga Buhari

Da gyara a jawabinka na sabuwar shekara; Dattijan arewa sun aika sako ga Buhari

- Kugiyar dattijan yankin arewa maso gabas sun bayyana jawabin shugaba Buhari na sabuwar shekara a matsayin fanko

- A wani bayani da ta fitar ranar Talata, kungiyar ta ce 'yan Nigeria sun yi tsammanin zai sanar da sauke shugabannin rundunonin tsaro

- Kazalika, sun zargi shugaba Buhari da kin yin magana a kan batutuwan da suka fi addabar jama'a

A yau, Talata ne, dattijan Arewa suka yi kira da murya mai ƙarfi ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da ya gaggauta sauke shugabannin tsaron ƙasar nan kamar yadda doka ta tanada.

A cewar dattawan, "naɗin kafatanin shugabannin tsaron ya saɓawa doka kuma kuskure ne da hakan na iya ci-gaba da haifar da masu laifi da yan bindiga."

Cikin bayaninsu, manyan arewa a ƙarƙashin haɗakar ƙungiyar dattawan arewa maso gabas, sun bayyana sakon shugaban ƙasa a matsayin fanko sakamakon ƙin sanar da sauke shugabannin tsaro a cikinsa.

KARANTA: NIMC ta kirkiro manhajar katin dan kasa a kan wayoyin hannu

Sakon na cewa, "sanar da sauke jagororin tsaron ƙasar nan shine babban albishir da shugaban ƙasa zai yi ga yan Najeriya su yi murna.

Kungiyar arewa ta gabatar da sabbin bukatu uku wurin shugaba Buhari a 2021
Kungiyar arewa ta gabatar da sabbin bukatu uku wurin shugaba Buhari a 2021 @Daily_trust
Asali: Twitter

"Mutane da yawa na mutuwa kullum sakamakon hare-haren na yan ta'adda a arewa sai dai ba'a kawo rahoton hakikanin abinda ke faruwa.

KARANTA: 2023: Guguwar sauyin sheka ta sake dawowa majalisar wakilai

"Mun saurari jawabin shugaban ƙasa da kunnen basira da tsammanin zai wani gagarumin albishir na sabuwar shekara, sai ga shugaban ƙasar ya ba da mu inda ya ƙi taɓo muhimman abubuwan da suka kamata."

A kwanakin baya ne Legit.ng ta rawaito gwamnan Babagana Umara Zulum, na cewa tsaro ya karu a jihar Borno a karkashin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, duk hare-haren da ake kai wa a kwanakin baya bayan nan.

Farfesa Zulum, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da ya karbi bakuncin kungiyar dattijan arewa a karkashin jagorancin shugabanta, Ambasada Shehu Malami, da kuma sakatarenta, Audu Ogbeh.

Hakan na kunshe ne a cikin jawabin da gwamnatin jihar Borno ta fitar ranar Litinin mai taken 'Zulum: Duk da kashe-kashe, shaidu a kasa sun nuna cewa an fi samun zaman lafiya a karkashin mulkin Buhari a Borno.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng