Hukuncin kuskure: Za a biya wani mutum N3.7bn bayan kwashe shekaru 28 a gidan kurkuku

Hukuncin kuskure: Za a biya wani mutum N3.7bn bayan kwashe shekaru 28 a gidan kurkuku

- Daga bisani gaskiya ta yi halinta kuma na tabbatar da adalci a kan wata shari'ar bakar fata a Amurka

- Bisa kuskure aka yankewa Chester Hollman III hukuncin kisa sakamakon kisan wani mutum a yayin da yake da shekaru 21 a duniya

- A yanzu bayan ya kwashe shekaru 28 a gidan kurkuku an gane ba shi da laifi kuma za a biya shi N3.7bn a matsayin diyya

Wani mutum dan asalin Philadelphia ya samu 'yanci a karo na biyu a rayuwarsa kuma ya koma cikin mutane bayan kwashe shekaru 28 a gidan kurkuku.

Chester Hollman III an yanke masa hukunci ne bisa kuskure kuma aka yanke massa hukuncin kisa duk da ba shi da laifi.

Amma kuma bayan shekaru 28 da aukuwar lamarin, an gane cewa bashi da laifi kuma an yanke hukuncin biyan shi N3.7bn a matsayin diyya.

KU KARANTA: Farashin hatsi: Bude iyakokin tudun kasar nan ya ragargaza farashin kayan abinci

Hukuncin kuskure: Za a biya wani mutum N3.7bn bayan kwashe shekaru 28 a gidan kurkuku
Hukuncin kuskure: Za a biya wani mutum N3.7bn bayan kwashe shekaru 28 a gidan kurkuku. Hoto daga Netflix
Asali: UGC

Chester mai shekaru 21 ya kasance direba. An kama shi wata rana a tsakar garinsu inda aka zargesa da hannu a cikin fashi da makamin da yayi sanadiyyar rayukan jama'a.

A 2020, alkali ya wanke Chester sannan ya bada umarnin biyansa N3.7bn na irin halin da aka jefa shi ciki da bata masa lokacin rayuwarsa da aka yi.

KU KARANTA: Bidiyon Kakan da ya kai jikonkinsa gwajin DNA, ya gano ba shi ya haifa mahaifinsu ba

A wani labari na daban, 'yan bindiga masu tarin yawa sun cimma ajalinsu sakamakon samamen tudu da na jiragen yaki da soji suka kai musu a Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun a jihar Kaduna, Vanguard ta wallafa.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar ya ce dakarun sun tabbatar da samamen da suka kai a ranar Litinin a Albasu, Rahama, Sabon Birni, Rikau, Fadama kanauta, Galadimawa, Kaya, Kidandan, Yadi, Dogon Dawa, Ngede Allah, Damari, Saulawa, Takama, Kuduru, Ungwan Yakoda babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari.

"An ga 'yan bindiga a Yadi kuma an ragargaji yankin ta sama sannan an kashesu da yawansu," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel